A cigaba da kokarin bunkasa fasahar zamani da samar da ayyukan yi ga matasa, mai girma ministan sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, Shaik, Dakta, Isah Ali Ibrahim Pantami (FNCS, FBCS, FIIM) ya ɗora tubalin fara gina katafariyar cibiyar kirkire-kirkire da ayyukan yi na fasahar zamani ta kasa gabaɗaya, (National Digital Innobation And Entreprenuership Centre) a birnin tarayya, (Abuja) a wannan rana.
A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2020, mai girma Shugaban kasa, Muhammadu Buhari (GCFR) ya amince a samar da cibiyar bayan da mai girma minista, Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami ya gabatar da kudirin tare da amsa tambayoyi kimanin guda 22 cikin nasara a ya yin zaman majalissar zartarwa (FEC Meeting).
Bugu da kari, tunanin samar da cibiyar, ya samu goyon bayan kafatanin ƴan majalissar zartarwa na fadar Shugaban kasa la’akari da ɗumbin tasiri da gudunmawar da cibiyar za ta bayar ga cigaban Nageriya da ƴan Nageriya gabaɗaya.
Baya da haka, mai girma minista, Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami, ya umarci mai girma shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwar zamani ta kasa (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi (CCIE) da ya sanya batun samar da cibiyar a cikin tanadin kasafin kuɗin hukumar. Inda daga bisani kuma majalissar kasa ta amince da bukatar domin amfanin kasa.
Haka zalika, cibiyar za ta taimaka wajen sanya jama’a su rungumi amfani da fasahar zamani da kuma samar da managartan manhajoji akan ilimin gyare-gyaren kayan fasaha da zamantakewar al’umma.
Baya da haka, cibiyar za ta taimaka akan tsarin fara kasuwanci da kuma samar da sabbin fasahohi da dabaru waɗanda za su taimaka wajen samar da ayyukan yi da rungumar sana’o’in dogaro da kai gami da ɗabbakawa da bunkasa fasahar sadarwar zamani haɗi da sauran damammaki na kyautata hanyoyin nazari da bincike da haɗakar bitar karawa juna sani kan samar da kyakkyawan yanayi.
A cikin jawabin da ya gabatar a ya yin da ya ke ɗora harsashin fara ginin cibiyar, mai girma ministan sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami, ya yi godiya gami da yabo da jinjina ga mai girma shugaban kasa, kana kuma Baban tattalin arzikin fasahar zamani, Malam Muhammadu Buhari (GCFR) a dangane da irin cikakken haɗin kai da goyon bayan da ya bayar wajen tabbatuwar wannan aiki da ma sauran ayyuka.
Daga nan mai girma minista, Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami, ya jinjinawa mai girma shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwar zamani ta kasa (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi (CCIE) dangane da irin namijin kokarin da ya yi wajen ganin an fara aiwatar da tsarin tattalin arziki na fasahar zamani (National Digital Economy Policy). Inda ya kara da bayyana rawar da hukumar ta (NITDA) ta ke takawa a matsayin gagaruma tare da kara zaburar da hukumar akan ta cigaba da goyon bayan bunkasa harkokin kirkire-kirkire da dabarun dagaro da kai a wannan kasa.
Daga nan mai girma minista ya kuma yi tilawar irin managartan nasarorin da Nageriya ta ke samu ta hanyar ma’aikatarsa ta sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, kamar gudunmawar kaso goma sha bakwai da ɗigo tamanin da uku (17.83%) da kimiyyar fasahar sadarwar zamani ta bayar akan kididdigar kayayyan da Nageriya ta samar (GDP) a zango na biyu na shekarar (2020) kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar.
Gami kuma da horo daban-daban ta hanyar fasahar zamani da aka bayar waɗanda ƴan Nageriya sama da mutum (120,000) su ka amfana da tsare-tsare na kyautata hanyoyin sadarwa da sauran tsare-tsare da dama.
Taron aza harsashin fara ginin cibiyar ya samu halartar shugaban kamfanin mai na kasa, (NNPC), Malam Mele Kyari, da shugaban (Galady Backbone), Farfesa Muhammad Abubakar da shugabar hukumar sadarwa ta tauraron ɗan adam, Mista Abimbola Alale, gami da sauran manyan baki da dama daga ma’aikatun gwamnati da hukumomi masu zaman kansu. Daga karshe, mai girma minista, Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami ya gode musu gabaɗaya bisa amsa wannan gayyata da su ka yi ya aza tubalin fara ginin wannan cibiya a yau.