Patience Jonathan Tsagera Ce –Tsohon Ambasadan Amurka

Daga Abubakar Abba

Tsohon Ambasadan ƙasar Amurka a Najeriya John Campbell ya danganta matar tsohon shugaban ƙasar Najeriya Patience Goodluck Jonathan, da jahilci da son nuna jin daɗin rayuwa lokacin da mijin ta ke kan karagar mulki.

Campbell ya bayyana hakan ne a rubutun da ya yi ya kuma yaɗa shi a yanar Gizo ta cibiyar huɗɗar jakadancin ƙasa da ƙasa. ya nuna mamakin sa a kan yadda Patience ta kuɗance, ganin cewar ta shafi yawancin rayuwar ta a matsayin ma’aikaciyar gwamnati, Campbell ya ci gaba da cewa Patience mace ce da kowa baya son halin ta, inda ya koka a kan yadda har yanzu ba a yanke mata hukunci ba, a kan laifukan da ta tabka ba. Ya kuma ce, “abin da ban tsoro ga wanda ya shafe rayuwarsa a matsayin ma’aikacin gwamnati, har ya mallaki Dalar Amurka Miliyan 35 a ƙasa kamar Nijeriya.” In ji shi.

Tsohon Ambasadan ya ce, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), a yanzu tana kan bincikar Patience ta kuma rufe asusun da take ajiya a bankuna huɗu, sannan kuma ta karɓe ƙaddarorin ta.

Wasu daga cikin matakan da EFCC ɗin ta ɗauka, ya haɗa da rufe Asusun da aka ajiye Dalar Amurka Miliyan 35.

Patience ta kuma yi iƙirarin cewar, EFCC  kulle Asusun Bankin wanda na ‘yan’uwanta ne da na mahaifiyarta da ta mutu har da nata na kanta.

Ta zargi hukumar a kan ƙulla yaƙi da ita don ta mara wa mijinta baya lokacin yaƙin neman zaɓensa a shekaar2015.

Campbell  da yake tsokaci a kan yaƙi da cin-hanci da rashawa na shugaba Muhammadu Buhari ya ce akwai ci baya  musamman a kan ‘yan’adawa, ganin wasu na zargin cewar Buhari ya na yin amfani da EFCC wajen  yaƙar maƙiyyansa ‘yan siyasa.

Ya ce a abin da ake yaɗa wa, musamman a wasu sassan ƙasar nan inda Kiristoci suka fi yawa, ana amafnin da damar yaƙi da cin-hanci da rashawa don misilanatar da Nijeriya.

Kwamitin mai karɓar koke da ke majalisar wakilai ya bada takarda da a kamo shugaban riƙo na EFCC Magu saboda ƙin gurfana a gaban kwamitin saboda koken da Patience ta rubuta wa kwamtin.

Yunƙurin kwamitin wani wakili a majalisar kuma Kirista ɗan PDP daga Kudu ne ya gabatar da a kamo Magun.

A cewar sa, abin ya zama kamar gado a ƙasar nan inda shugabanin ƙasa kan yi amfani da EFFC  da wasu hukumomi na yaƙi da cin-hanci da rashawa don muzguna wa ‘yan adawa.

Tabbas haka ne a ƙarƙashin mulkin Buhari, ma fi yawancin manyan mutanen da da ake bincike a kan cin-hanci da rashawa ‘yan PDP ne da suka yi aiki ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasa Jonathan, inda ma fi yawancin su kiristoci ne daga kudancin ƙasar nan.

Exit mobile version