Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Patrick Nip Tak-Kuen: Dokar Tsaron Kasa Ta HK Za Ta Kyautata Manufar Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu

Published

on

Shugaban hukumar kula da harkokin jami’an gwamnatin yankin Hong Kong, Patrick Nip Tak-kuen ya zanta da wakilin CMG a jiya Juma’a, inda ya bayyana cewa, makasudin gwamnatin kasar Sin na kafa dokar tabbatar da tsaron kasa a yankin Hong Kong shi ne, nuna kulawa ga al’ummun yankin, don haka dokar tana da babbar ma’ana ga wadata da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin, kuma za ta kara kyautata manufar “kasa daya mai tsarin mulki iri biyu” da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa.

Jami’in yana mai cewa, an kafa dokar ne domin gufanar da masu aikatawa laifuffukan lahanta moriyar kasa a gaban kuliya, tare kuma da kiyaye hakki da ‘yancin yawancin al’ummun kasar.
Ya kara da cewa, kwamitin tsakiya na JKS yana dukufa kan aikin tabbatar da manufar “kasa daya mai tsarin mulki iri biyu” a yankin musamman na Hong Kong, haka kuma yana goyon bayan daukacin matakan da gwamnatin yankin ta dauka domin ingiza ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar al’ummu, shi ya sa idan aka cimma burin tabbatar da tsaron kasa a yankin, ko shakka babu za a aiwatar da manufar “kasa daya tsarin mulki biyu” a Hong Kong yadda ya kamata.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai