Khalid Idris Doya" />

Paul Biya Ya Sakin Fursinoni 333 A Kamaru

  Shugaban Kamaru Paul Biya ya ba da umarnin sakin wasu Fursinoni 333 wadanda aka tsare saboda zarginsu da alaka da masu fafutikar ballewa daga kasar.

Wata sanarwa daga fadar shugaban ta ce an fasa gurfunar da mutanen a gaban kotun soji.

Wani jami’in gwamnatin kasar ta Kamaru ya bayyana a wajen wani taron manema labarai cewa suna kokarin sulhu bayan kwashe shekara uku ana rikicin da ya yi ajalin dubban mutane da kuma raba kimanin mutum 500,000 da muhallinsu.

Rikicin ya fara ne a lokacin da wasu lauyoyi da malamai suka fara yajin aiki dangane da amfani da Turancin Faransa a kotuna da makarantu a yankin da ke magana da Turancin Inglishi a yankunan Arewa-maso-Yammaci da kuma Kudu-maso-Yammacin kasar.

A watan Oktoban 2017, masu fafutika sun ayyana samun wani kwarya-kwaryar ‘yanci a yankunan biyu, wani abu da Shugaba Biya ya yi watsi da shi.

Daga nan ne wasu daga cikin masu fafutikar suka dauki makamai, abin da ya jawo arangama tsakaninsu da dakarun gwamnati.

Sai dai ba a san ko umarnin sakin fursinonin zai bayar da damar sakin manyan jagororin ‘yan awaren ba.

Firaministan kasar Joseph Dion Ngute ya ce, an dauki matakin ne domin kwantar da hankalin al’ummar kasar da rikicin ‘yan awaren ya raba kawunansu tare da haddasa asarar dimbin rayuka.

Kungiyar ‘International Crisis Group’ ta ce, mutane kusan 3,000 suka mutu sakamakon rikicin, yayin da sama da 500,000 suka tsere wa gidajensu, sannan wasu suka zama ‘yan gudun hijira a kasashe makwabta.

Wannan ya sa shugaba Paul Biya ya shirya taron kasa domin sasanta al’ummar kasar, amma ‘yan awaren da kuma ‘yan adawa sun kaurace wa taron muhawarar ta kasa.

‘Yan adawan sun gindaya sharadin cewa, sai an saki shugabansu, Julius Ayuk Tabe da magoya bayansa da aka yi wa daurin rai da rai kafin su shiga taron.

Mazauna yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi su ke da kashi daya bisa 5 na al’ummar Kamaru mai yawan mutane miliyan 24.

Akwai masu sharhi da ke ganin da wuya ‘yan awaren su yi maraba da sakin fursinonin wadanda suka kafe wajen ganin sun kafa kasar Ambazonia daga kasar Kamaru.

Exit mobile version