Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
An yi kira ga ‘yan siyasa da su ƙauracewa duk wani abin da zai kawo tashin-tashina ta hanyar furucinsu ko ayyukansu a ƙasar nan, Hakimin Wushishi, Alhaji Shehu Ibrahim wanda ya samu wakilcin Mai Yaƙin Wushishi, Alhaji Abba ne ya yi kiran a lokacin da shugaban jam’iyyar na jihar Neja, Kwamared Musa Adamu Nasko ya ziyarce shi a fadar shi.
Alhaji Shehu ya ci gaba da cewar siyasa wata hanya ce ta kawo ma ƙasa ci gaba ba koma baya ba ta hanyar ƙuri’a, don haka duk ɗan siyasar da ke son kwarjini da amincewar jama’a, to lallai ya kusanci mutanen nan cikin hikima da dubara, duk ɗan siyasar da ya zama mai farraƙa kawunan jama’a ya jefa su cikin ƙunci, lallai wannan ba masoyinsu ba ne na asali.
Bayan barin fadar Hakimin, shugaban na PDM ya buɗe ofishin jam’iyyar reshen Ƙaramar Hukumar Wushishi, da tabbatar da shugabancin jam’iyyar a matakin Ƙaramar Hukuma.
Da ya juya kan zaɓukan Ƙananan Hukumomi mai zuwa, a jihar Neja kuwa, ya ce kamar yadda suka sani tun farko haka ita ma Hukumar zaɓe ta jiha ta ayyana cewar zaɓukan Ƙananan Hukumomi na nan daram, ƙarshen Nuwamba zuwa Disambar wannan shekarar, kuma jam’iyyarsa ta shirya dan fafatawa da ita, a fagen fama, mazaɓu 1034 da ‘yankuna 74 da ke jihar nan za su baza komarsu dan ɗibar na su rabon, domin ko zaɓukan da suka gabata sun fafata, kuma sun samu nasara duk da cewar wasu sun karkatar, da kujerun da suka samu nasara zuwa aljihunsu.
Ya gabatar da ‘yan takarar kansuloli na yankin Wushishi su goma, da masu takarar majalisar dokokin jiha 2, mataimakin shugaban jam’iyar yankin Neja ta Arewa, Malam Awwal Goma ya ce bai da shakku daga takarar kansila, zuwa Ƙaramar Hukuma kai har ma ‘yan majalisu, da kujerar gwamna da sauran kujerun sai sun nema a jihar nan.
Dan haka magoya bayan PDM sun fito ƙwansu da kwarkwatar su, sun nuna goyon bayan ga shugabancin Kwamred Musa Adamu Nasko a matsayin shugaba, kuma za su yi duk mai yiwu wa wajen ganin jam’iyyar , tayi kafaɗa da kafaɗa da jam’iyya mai mulkin a ƙasar nan. Jama’a dai ake nema kuma muna da su, ƙuri’ar ka kuma ‘yancin ka, dan haka zamu yi amfani da ƙuri’un mu wajen tabbatar da, abin da muke fata.
Yanzu haka a jam’iyyance mun fito da wasu tsare-tsare, duk mai sha’awar yin takara sai mun zaunar da shi, ya faɗa mana manufofinsa a rubuce, mun yi yarjejeniya a rubuce, yana kaucewa mu kuwa lallai sai mun ga bayan kujerar nan. Dan haka ina tabbatarwa al’ummar Ƙaramar Hukumar Wushishi da sauran Ƙananan Hukumomi bakwai, na yankin Neja ta Arewa lallai jama’a su ba PDM haɗin kai da goyon baya su ga sabon salon siyasa a wannan ƙarni.