Connect with us

Uncategorized

PDP Da APC Zasu Kara A Zagaye Na Biyu A Jihar Osun

Published

on

Jam’iyyun PDP da APC zasu kara a zagaye na biyu na zaben jihar Osun, wanda aka soke sakamakon zaben na wasu yankuna, saboda abinda hukumar zaben ta kira da alamun tambaya.

Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP da abokin takarar shi Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC zasu sake karawa a zagaye na biyu don tantance gwani a tsakaninsu.

Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 254,698, yayin da Oyetola na jam’iyyar APC 254,345. Amma hukumar zaben ta ce zaben cike yake da kura-kurai wadanda ba zasu bari a bayyana wanene tsayayyen wanda ya lashe zaben ba, zuwa yanzu hukumar bata kai ga bayyana yaushe za a sake gudanar da zaben ba.

 

 
Advertisement

labarai