Sagir Abubukar" />

PDP Da PRP Sun Ki Amincewa Da Sakamakon Zaben Cike Gurbin Dan Majalisar Bakori A Katsina

Sun Nemi A Soke zaben mazabu shida

PDP da PRP

Jam’iyyun adawa na PDP da PRP a jihar Katsina, sun yi fatali da zaben cike gurbin da aka gudanar a ranar asabar din da ta gabata a karamar hukumar Bakori, inda hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa ta ayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Alhaji (Dr.) Aminu Ibrahim, ya samu nasarar.

Shugaban jam’iyar PDP na Jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri tare da hadin gwiwa dan takarar PRP, Abdullahi Isma’il suka bayyana matakin da suka dauka na garzayawa kotu domin neman hakkin su kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Alhaji Salisu Majigiri ya kara da cewa wannan sakamakon zaben, ba wanda al’ummar karamar hukumar Bakori suka zaba ba ne. An zo an nuna karfin gwamnati, tun daga kakakin majalisar dokoki na jihar Katsina da yan majalisa kasa da sakataren gwamnati jihar Katsina da shugabanni kananan hukumomi da manyan sakatarori daban daban, a ranar Katsina ta tsaya cik, sai ya za’a yi a kwaci karamar hukumar Bakori ta hanyar sayen kuri’u.

Majigiri ya ci gaba da cewa hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa ta ayyana cewa mu Jam’iyyar PDP ta samu kuri’u dubu goma sha daya da dari ukku da hamsin da shidda, APC ta ci dubu ashirin da dari hudu da ashirin da biyar. To wannan sakamakon muna kalubalantar shi, dalili kuwa akwai cibiyoyin jefa kuri’u sittin da daya, wadanda suka yi batan dabo. Karamar Hukumar na da cibiyoyin jefa kuri’u dari biyu arba’in da biyu, amma sai hukumar zabe ta ce mana dari da tamanin da daya aka maida su. Bayan sakamakon ya fito mu ke zargin akwai bukatar a bincika. Kuma mun tantance mun ga mazabu shidda ne abun ya faru akwai Kurami Dankwani da Barde Kwantakwaram da Kabomo da Bakori A da Tsiga da kuma mazabar Guga. Wanda idan aka tattara masu jefa kuri’un, sun kai dubu saba’in da hudu da dari takwas da tamanin da hudu, anan ne aka ce dan takarar mu ya samu kuri’u dubu shidda da arba’in da bakwai, ita kuwa jam’iyar APC dan takarar ta ya samu kuri’u dubu sha ukku da tamanin da Tara, anan ne muke kalubalantar wannan sakamakon zaben kuma za mu bi dukkan wani mataki na shari’a don mu kwato hakkin al’ummar karamar hukumar Bakori da suka zabi Jam’iyyar PDP aka yi mana magudi. Muna son a soke zaben wadannan mazabu shidda a sake zabe.

Exit mobile version