PDP Na Kawo Cikas Ga Kokarin Gwamnatin Na Kawo Karshen Rikicin Manoma Da Makiyaya – Fadar Shugaban Kasa

Kudu Da Arewa

Fadar shugaban kasa ta ce gwamnonin PDP na kawo cikas ga kokarin gwamnatin tarayya na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da ya ke janyo hasarar dukiyoyi da rayuka.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa martani da ya fitar ranar Laraba biyo bayan taron gwamnonin PDP a Jihar Akwa Ibom, ranar Litinin.

Haka kuma, Garba Shehun ya zargi gwamnonin na PDP kan kin bada hadin kai na ganin kananan hukumomi sun koma aiki daidai kamar yadda ya ke a cikin kundin dokoki.

“Hanyoyin da aka kawo za su samar da mafita ga matsaltsalunda garuruwa da dama su ke fusknata a kasar, amman gwamnonin PDP su ka ki bada goyon baya,”in ji shi.

Har wa yau, ya zarge su da nuna banbanci da bangaranci a tsakanin ýan Najeriya tare da sa iyaka ga wasu na gudanar da ayukkansu a wasu jihohin.

“Haka kuma, mai ya sa sai yanzu gwamnonin su ke neman hadin kan kowane bangare a jihohinsu, mai ya hana ba su yi hakan ba  a baya?

A cikin sanarwar, Shehu ya ce gwamnonin ba su samar da kowace iirn mafita ga kasar ba a lokacin annobar kwarona da kuma matsalar tattalin arzikin da aka fuskanta. Ya kuma yi Allah-wadai da su kan kin goyon bayan haramta Tiwita, wanda ya ce su na anfani da shafin wurin yada labarun karya.

 

 

 

 

Exit mobile version