PDP Ta Amince Wa Gwamnan Nasarawa Ya Yi Tazarce A Zaben 2023   

Membobin

Daga Yusuf Shu’aibu,

Jam’iyyar PDP a karamar hukumar Akwanga da ke Jihar Nasarawa, ta amince wa Gwamna Abdullahi Sule ya yi tazarce a karo na biyu a kan kujerar gwamna.

Wani dan majalisa da ke wakiltar mazabar Akwanga ta Kudu a majalisar Jihar Nasarawa karkashin tutar jam’iyyar PDP, Hon Samuel Tsebe shi ya bayyana hakan a wannann mako a karamar hukumar Akwanga lokacin da ake gudanar da ake taron masu ruwa da tsaki na shuwagabannin jam’iyyu da kuma rukunin kungiyoyin addini a karamar hukumar. Tsebe ya bayyana cewa, a nasa ra’ayin yana bukatar gwamnan jihar ya samu nasara a babban zaben shekarar 2023, bisa nasarorin da ya samu a cikin jihar musamman ma a karamar hukumar Akwanga.

Ya yaba wa Gwamna Sule bisa irin shugabancin da yake gudanarwa a cikin jihar wajen bankasa ababen more rayuwa, wanda za a iya tabbatar da haka idan aka duba yawan hanyoyin da aka gida a fadin jihar musamman ma a karamar hukumar Akwanga. Haka kuma, dan majalisar karkashin tutar jam’iyyar PDP ya ci gaba da bayyana cewa, ya amince da yadda gwamna yake kashe kudade ta hanyar da ta dace a cikin jihar tun daga wajen biyan ma’aikata albashi da kuma tsofaffin ma’aikata masu amsar fansho.

Shi ma mataimakin shugaban majalisar Jihar Nasarawa, Hon Tsentse Dandaura, wanda yake wakiltar mazabar Akwanga ta Yamma karkashin inuwar jam’iyyar APC, ya bukaci mutanen karamar hukumar Akwanga da su goyi bayan Gwamna Sule, bisa ayyukan ci gaba da ya yi musu a wannan mazaba ta Akwanga.

Exit mobile version