Connect with us

SIYASA

PDP Ta Ba Obaseki Damar Shiga Zaben Fidda Gwani

Published

on

Jam’iyyar adawa ta PDP ta amince gwamnan jihar Edo Godwin Obasaki wanda ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki da ya tsaya takarar a zaben fitar da gwani da zai gudana a karshen watan nan.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, PDP ta ce la’akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta, Gwamna Obasaki na da damar tsayawa takarar fitar da gwani a zaben gwamnan jihar.

Haka zalika kwamitin koli na PDP wanda shi ne ke kan gaba wajen tabbatar da bin tsarin jam’iyyar ya ce mataimakin gwamnan Philip Shu’aibu shi ma yana da damar shiga a dama da shi wajen zaben zama mataimakin gwamnan.
Advertisement

labarai