PDP Ta Bukaci Jami’an Tsaro Su Kara Jajircewa Wajen Yaki Da Ta’addanci A Sakkwato

Ta'addanci

Jam’iyyar PDP a jihar Sakkwato ta bukaci hukumomin tsaro su kara tashi tsaye wajen magance matsalolin sha’anin tsaro da suka hada da ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane a Sakkwato da makwabtan jihohi.

 

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Sakkwato, Hon. Bello Goronyo ne ya yi wannan kiran a ziyarar aiki da ya jagoranci kwamitin zartaswar jam’iyyar a wajen Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Mustapha Abubakar a Yanki na 10 a jiya.

 

Goronyo ya yabawa kokarin da jami’an tsaro ke yi wajen yaki da ta’addanci tare da kira gare su da su kara jajircewa wajen shawo kan bahaguwar matsalar musamman a a wannan lokacin da ake samun yawaitar garkuwa da mutane a sassan jihar.

 

Shugaban Jam’iyyar ya tabbatarwa Mataimakin Sufeto-Janar, cikakken hadin kan da goyon bayan jam’iyyar wajen samar da zaman lafiya a fadin Jihar. Ya ce ziyarar na da manufar karfafa hadin kan da ke tsakanin jam’iyyar da Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar.

 

A jawabinsa Mataimakin Sufeto-Janar, Mustapha Abubakar ya bayyyana cewar za su ci-gaba da kokarin da suke yi ba dare ba rana domin kawo karshen matsalolin tsaro a Jihar da yankin Sakkwato bakidaya.

 

Shugaban Jam’iyyar ya kuma kai irin wannan ziyarar wajen Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Sani Ka’oje da Shugaban Rundunar Tsaro ta (NSCDC) wadanda duka jam’iyyar ta yabawa hobbasar kwazosu da bukatar kara daura damara domin samar da zaman lafiya mai dorewa a Jihar.

 

A wani lamarin kuma, Jam’iyyar PDP a Jihar ta gabatar da kyautar kudi ga Kiristoci domin su gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin sauki da walwala.

Exit mobile version