PDP Ta Dage Babban Gangamin Yakin Zabenta A Abuja

Babban jam’iyyar adawa a Nijeriya (PDP) ta dakatar da gangamin gangankon yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da ta tsara gudanarwa a cikin babban birnin tarayya Abuja a jiya Asabar 9 ga watan Fabrairun 2019.
A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Daraktan yada labarai na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na PDP, Mista Kola Ologbondiyan wanda ya rabar a jiya, PDP ta ce, daukan matakin jinkirta babban gangamin nata ya biyo bayanin hanasu amfani da muhallin wajen da za su yi gangamin ne.
A cewarsa: “PDP ta biya kudin haya da samun amincewar muhallin a hukumance domin gudanar da babban gangamin yakin neman zabenmu a filin Old Parade Ground, Garki, Abuja.” sai dai ya bayyana cewar duk da hakan, an hanasu wannan muhallin domin gudanar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar.
Ologbondiyan ya yaba wa ‘yan Nijeriya a bisa kokarin halartar wannan babban gangamin na jam’iyyar PDP da ta tsara yi a Abuja.
“Muna tir da wannan lamarin, da zarar muka sanya sabon ranar gudanar da wannan gangamin zamu sanar nan gaba kadan,” in ji shi.

Exit mobile version