Daga Khalid Idris Doya
Jam’iyyar PDP reshen jihar Neja ta dakatar da tsohon gwamnan jihar, Dakta Muazu Babangida Aliyu bisa zarginsa da riddar siyasa (wato Anti-party a turance) ga harkokin jam’iyyar.
Sun dakatar da tsohon gwamnan ne a yayin wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da suka gudanar a karamar hukumar Chanchaga da ke Minna a ranar Litinin.
PDP ta kuma zargi tsohon gwamnan da yi mata zagon kasa tare da yin aiki wa jam’iyyar APC a yayin babban zaben 2015 ta karkashin kasa, su na masu karawa da cewa ba ya halartar taron jam’iyyar ko wasu harkokinta.
Taron wanda ya samu halartar shugabannin jam’iyyar a gundumomi 8 daga cikin 11, tare da dattawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a karamar hukumar Chanchaga.
Wani hadimin yada labaran tsohon gwamnan, Dakta Mu’azu, Mista Bala Bitrus, ya bayyana cewar wannan dakatarwar da aka yi, abun dariya ne tsagwaranta, yana mai cewa PDP sun rasa dalilin da za su fake da shi wajen aiwatar da abun da suka yi niyya ne kawai.
Ya ce, ganawar da aka yi din haramtacciya ce, kuma Aliyun zai yi bayani da zarar ya amshi sakon dakatar da shi.