Sani Hamisu" />

PDP Ta Kafa Kwamatin Bincike Kan Rashin Nasararta A Zaben ‘Yan Majalisu

Kwamatin Amintattun PDP na Kasa, ya kafa wani Kwamitin binciken kwakwaf don bankado gaskiyar al’amarin da ya faru bisa zargin da ake yi wa wasu daga cikin Mambobinta dangane da irin rawar da su ka taka wajen hadin baki da Malaman  zabe a lokacin zaben ’Yan Majalisar Tarayya na kasa da aka gudanar a watan Mayun wannan shekara.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar PDP ta kasa, Mista Kola Ologbondiyan a makon da ta gabata a Abuja. Kamar yadda Ologbondiyan ya bayyana, tsohon Shugaban Majalisar Dattijan Nijeriya, Sanata Adolphus Wabara shi ne Shugaban Kwamatin, Farfesa Wale Oladipo kuma a matsayin Sakatarensa.

Sauran Mambobin sun hada da Sanata Ibrahim Mantu, Sanata Stella Omu, Mista Austin Opara, Sanata Abdul Ningi da kuma Madam Margaret Icheen.

Babban aikin wannan Kwamati kamar yadda Babban Sakataren Yada Labaran nasu na kasa ya bayyana shi ne, sanin jinjinan makasudin da ya sanya mahukuntan Jam’iyyarsu ta PDP su ka bijire wa matsayar da Jam’iyya ta cimma a daidai lokacin zaben ‘Yan Majalisar Tarayya ta kasa da ya gabata. Kazalika, a kuma yi kokarin bincike ko gano ko akwai sa hannun Jam’iyya wajen yanke hukuncin Mambobin da ke da wannan hannu a cikin al’amarin, in ji shi.

“Don samun tabbacin ko dai akwai wasu kwararan dalilai dangane da wannan mataki da wadannan Mambobin su ka dauka, ko shakka babu wannan Kwamati zai bincika ya kuma tabbatar don samun jituwar da ta dace a Siyasance da kuma tattaunawa da Sanatoci tare da sauran ‘Yan Majalisar Wakilanmu na kasa.

Haka zalika, da zarar an yi nasara wajen yin wannan bincike tare da bankado muhimman abubuwan da suka kamata, akwai tabbacin cewa a nan gaba kadan abubuwa za su yi kyau, sannan sauran ‘Yan Jam’iyya za su ci gaba da kare muradan Jam’iyyar tamu a ko’ina suke a fadin wannan kasa,” a cewar tasa.       

Haka zalika, a fadin na Ologbondiyan, an baiwa wannan Kwamati mako uku kadal daga lokacin da aka rantsar da Shugabanninsa don kawo cikakken rahoton cikakken sakamakon da ya samu.

Idan ba a manta ba, a 11 ga watan Yuli ne ana dab da rantsar da Majalisa ta 9, Jam’iyyar PDP ta bayar da sanarwar cewa, Sanata Ali Ndume ne Dan takararta na Shugabancin Majalisar Dattijai, Umar Bago Kuma a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai ta kasa

Kamar yadda Jam’iyyar  ta bayar da wannan sanarwa ta bakin Babban Sakataren nata na kasa Sanata Umar Tsauri, cewa ya yi an samu wannan matsaya ne bayan kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyya, manya-manyan Shugabanni, Gwamnoni, zababbun Sanato da kuma sauran ‘Yan Majalisar Tarayya na Jam’iyyar tasu ta PDP.

Tsauri, ya kara da cewa, wannan matsaya da suka dauka ta yi daidai da abin da sauran ‘yan’uwansu ‘Yan kasa nagari suka amince da shi, musamman idan aka yi la’akari da kudire-kudiren da jam’iyyar tasu ke da shi don samun nasarar dorewar wannan demokradiyya da kuma tabbatar da ganin cewa ‘Yan Majalisar sun ci gaba da samun karfi tare da cin gashin kansu a Majalisa.

Duk da cewa, Dan takarar Jam’iyyar APC ne, Sanata Ahmed Lawan ya dare kan kujerar Shugabancin Majalisa Dattijan, Femi Gbajabiamila kuma ya zama Shugaban Majalisar Tarayya, sabanin yadda ita Jam’iyyar PDP ta ayyana.

Exit mobile version