Sanata mai wakiltar kudancin jihar Adamawa, a majalisar dattawa ta kasa Sanata Ishaku Abbo, ya bayyana jam’iyyar PDP da cewa ta mutu murus a jihar Adamawa.
Abbo, wanda ke magana lokacin da yake ganawa da jama’ar yankin muzabun kananan hukumomi Mubi ta kudu, Mubi ta arewa, Maiha, Michika, da kuma Madagali, a bukin kirsimeti da na sabon shekara, babu abinda PDP ta tsinana tunda ya fice.
Ya ci gaba da cewa “zamu dawo da jam’iyyar APC kan karagar mulki a zaben 2023, lokacin mulkin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, zai kare a 2023.
“Saboda da haka, ina kira ga jama’a da su fice daga PDP su rungumi jam’iyyar APC, domin kuwa shugaba Muhammadu Buhari, ya bada kwangilar aikin hanyar Samiya zuwa Bukula.
“Shugaba Buhari ya nuna min takardar amincewar, kwanannan kamfanin zaizo ya fara dubawa, za a yi muku hanya mai inganci domin ku rika gudanar da harkokin kasuwancinku” inji Abbo.
Sanata Elisha Abbo, ya ce Mubi yanki ne da ya shahara da harkokin Kasuwanci, da’ake kasuwancin kasa da kasa, ya ce aikin hanyar zai taimaka wajan gudanar da kasuwancin ba tare da wata matsala ba.
Ya kuma nuna damuwa da yadda ayyukan kungiyar boko haram ya maishe da tattalin arzikin yankin baya, ya ce zaiyi iya bakin kokarinsa na ganin harkoki sun koma daidai a yankin.