Connect with us

LABARAI

PDP Ta Nada Okowa A Matsayin Shugaban Kwamitin Shirya Babban Taronta Na Kasa

Published

on

Jam’iyyar PDP ta nada gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin shugaban kwamitin da zai shirya babban taron Jam’iyyar na kasa domin shirin tunkarar babban zaben 2019.

Mataimakin shugaban Jam’iyyar na kasa, Yomi Akinwunmi, ne ya kaddamar da kwamitin a madadin shugaban Jam’iyyar, Uche Secondus, a Sakatariyan Jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

Da yake godewa shugaban Jam’iyyar kan nadin da aka yi masa, Okowa ya tabbatar masu da cewa za su shirya babban taron a bisa turban gaskiya da adalci.

“Duk cikanmu, mun yi amanna da hadin kan Jam’iyyar, abin da muke da bukata a halin yanzun shi ne, gudanar da zaben fitar da gwani a bisa turban gaskiya da adalci ga dukkanin ‘yan takaran, ko ma dai a ina ne za a gudanar da taron, za mu yi abin da ya dace ne ta yanda ba wanda zai yi wani korafi, muna kuma da tabbacin za mu iya yin hakan.

“A matsayin mu na Jam’iyya, mun san mawuyacin halin da muke a cikin sa a kasarnan, wannan kuma shi ne babban aikin da wannan Jam’iyyar za ta dora wa wani a wannan shekarar, a wajen wannan babban taron za mu tabbatar da mun zaba wa kasarnan da wanda ya fi dacewa ya shugabance ta a karo na gaba, muna ma Allah godiya kan yadda Ya karfafa mana Jam’iyyar namu da mutanan da suka cancanci rike wannan mukamin.

“In har muka gudanar da zaben na fitar da gwani a bisa turban gaskiya da adalci, za mu samu hadin kan dukkanin ‘yan takaran wanda hakan zai kai mu ga samar da hadin kai a wajen yakin neman zaben namu.

“Za mu yi duk abin da ya dace, tare da taimakon Allah, za mu fitar da dan takara a tafarkin yin gaskiya da adalci, wanda ba wanda zai koka da komai.

A na shi jawabin, Akinwunmi, cewa ya yi an zabi gwamnan na Jihar Delta ne a matsayin shugaban kwamitin shirya babban taron, saboda matsayin sa na mutumin kirkin da ya shirya babban taro mafi tsaftan da aka gudanar da shi a dandalin, Eagle Skuare.

An bayyana tuta ta musamman wacce za a yi amfani da ita a wajen babban taron, hakanan kuma an baiwa dukkanin wakilan kwamitin shirya taron takardun su na kama aiki, inda Gwamna Dabe Umahi, na Jihar Ebonyi, ya kasance sakataren kwamitin.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: