Umar A Hunkuyi" />

PDP Ta Nada Saraki A Matsayin Daraktan Kamfen Din Atiku

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya zama sarkin yakin dan takaran shugabancin kasar nan a karkashin tutar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Kakakin Jam’iyyar ta PDP, Kola Ologbondiyan,ne ya bayyana nadin da aka yi wa Saraki din a matsayin babban daraktan kungiyar kamfen din ta neman shugabancin na Atiku.

Saraki yana daya daga cikin mutane 11 da suka fafata da Atiku wajen neman Jam’iyyar ta PDP ta tsayar da su takarar a babban zabe na 2019. Bayan da Atiku ya lashe zaben fitar da gwanin ne sauran ‘yan takarar suka yi alkawarin goya ma shi baya a bisa yanda suka ga an gudanar da zaben ba tare da wata hatsaniya ba.

Saraki zai yi aiki ne da sauran ‘yan takaran shida da kowannen su zai lura da shiyyar kasar nan guda a wajen yakin neman zaben.

Sauran masu kula da sassan shida sune, Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, wanda zai jagorancin kamfen din a shiyyar arewa maso yamma, Gwamnan Jihar Ebonyi, Dabid Umahi, zai kula da shiyyar Kudu maso gabas, Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, zai jagorancin shiyyar arewa maso gabas, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, zai jagoranci rundunar kamfen din ne a shiyyar kudu maso kudu, Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, zai jagoranci kamfen din a shiyyar arewa ta tsakiya, sai Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, wanda zai jagoranci rundunar kamfen din a shiyyar kudu maso yammacin kasar nan.

Wata majiya ta kusa da Atiku ta tabbatar da cewa, Jam’iyyar ce ta zabi Saraki da ya zama daraktan kamfen din amma ba Atiku ba. Ta kuma tabbatar da cewa, daraktan kamfen din na Atiku, Gbenga Daniel, yana nan a matsayin daraktan kamfen din na Atiku.

“Kamar yanda muka ce ne tun da farko, ya zama tilas Jam’iyya ta nada nata jagororin kamfen din. Wannan kuma yana da bambanci da kungiyoyin kamfen na dan takara, wadanda suke a karkashin jagorancin Gbenga Daniel.

Kola Ologbondiyan, ya ce sauran nade-naden da za a yi a kungiyar kamfen din suna nan za su biyo baya, za a bayyana su kwanan nan.

 

Exit mobile version