Umar A Hunkuyi" />

PDP Ta Shigar Da Karar Nasarar APC A Zaben Gwamnan Jihar Osun

A jiya, Jam’iyyar PDP a Jihar Osun, ta shigar da kara kan nasarar da dan takaran Jam’iyyar APC, Alhaji ‘Gboyega Oyetola, ya samu a zaben gwamnan Jihar da aka yi kwanan nan.

Shugaban Jam’iyyar a Jihar, Mista Soji Adagunodo, shi ne ya jagoranci sauran shugabannin Jam’iyyar wajen shigar da karan a ranar Talata da yamma.

Dan takaran Jam’iyyar ta PDP, Sanata Ademola Adeleke, tuni ya yi watsi da sakamakon zaben, inda ya yi zargin an tafka magudi tare kuma da koran magoya bayansa a rumfunan zaben da makamantan hakan.

Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan shigar da karan a babbar kotun Jihar da ke Osogbo, Adagunodo, wanda ke tare da sauran shugabannin Jam’iyyar ta PDP, cewa ya yi, Jam’iyyar tana da karfafan hujjoji na kalubalantar nasarar dan takaran na APC.

Da aka yi ma shi tambaya a kan abin da suke neman kotun ta yi masu, Adagunodo cewa ya yi, duk wannan sirri ne. Lauyoyin mu suna yin aiki tukuru don ganin an yi hukunci a kan lamarin.

Exit mobile version