PDP Za Ta Bayar Da Mamaki A Zaɓen 2019 -Gwamnan Enugu

Daga Sabo Ahma

A wata Magana da ake ganin kamar sharer fage ce ga tsaya wa takarar shugaba jam’iyyar PDP na ƙasa da tsohon ministan ilimi FarfesaTunde Adeniran,ke neman yi, gwamnan jihar Inugu Honarabul Ifeanyi Ugwuanyi, ya tabbatar wad a jam’iyyar cewa,  Farfesa Adeniran mutum ne wanda ked a cikakkiyar basirar gudanar da shugabancin jama’a a duk inda ya samu kansa.

Ya ce, “Kyakkyawar shaida da biyayyar da Adeniran ke wa jam’iyyar na nuna cewa matuƙar ya zama shugaba, abu ne mai sauƙi jam’iyyar PDP ta sake ƙwace mulkin ƙasar nan a shekara ta 2019”. Haka kuma Gwamnan ya ci gaba da bayyana Adeniran a matsayin mutum mai kyakkyawar manufa da ɗa’a da kuma kiyaye doka da oda. Saboda haka akwai tabbacin cewa jam’iyyar PDP za ta farfaɗo matuƙar ya zama shugaba.

Shi ma da yake nasa jawabin a lokacin ziyarara Adeniran, ɗin ya tabbatar da cewa, idan aka zaɓe shi a zaɓen da za a yi a watanDisamba ya zama shugaban jam’iyyar ta PDP zai tabbatar da cewa, dukkan matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar a baya, sun zama tarihi. Adeniran ya ce, yana cikin ‘yan takarar ne, saboda ƙoƙarin da suke na farfaɗo da ƙarfin jam’iyyar, yadda ‘yan Nijeriya za su sake zaɓarta kamar yadda suka yi a lokutan baya.

“A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar na san manufar da ta sa aka kafa ta. Jam’iyyarmu ita kaɗai ce jam’iyyar da aka kafa da manufar haɗa kan al’ummar ƙasa da bunsa tattalin arziƙin Nijeriya”. Na san za ku yard a da ni cewa taun da aka kafa jam’iyyara a shekara ta 1998, ta bayar da gudummawa a fannoni daban-daban na raya ƙasa da ci gaban rayuwar al’umma , baban ƙalubale da muke fuskanta wanda kuma shi ne ya yi sanadiyyar faɗuwarmu zaɓe shi ne na rashin tsayar da wanda jama’a ke so ya shugabance su.

Da yake mayar da jawabi a madadin tawagar da ta kai ziyarar Farfesa Jerry Gana ya gode wa gwamna Ugwuanyi bisa yadda ya zaɓo ‘yan tawagar, wadda ta ƙunshi, tsohonmaimakin shugaban Majalisar Dattawa Ibrahim Mantu, da Alhaji Shehu Gabam, da Ambasada Dakta Yemi Farombi da Sanata Ugochukwu Uba da Hajiya Zainab Maina, da sauran su.

Gana ya ce “Adenira mutum ne ya zzama abin koyi a siyasar Nijeriya, saboda haka muna tabbatarwa da gwamna da mutanen kudu-maso-gabas cewa, cewa wannan ɗantakarar da muka kawo maka talla tare da jama’arka cewa, izuwa yanzu babu wani ɗan takara day a kai kamarsa a jam’iyyar PDP. Saboda haka domin jam’iyyarmu ta sake farfaɗo wa muna buƙatar mutane irin su Adeniran da ke da kwarjinin jama’a su jagorance ta.

 

 

 

 

 

 

 

Exit mobile version