Daga Ibrahim Muh’d,
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano ta jaddada aniyarta ta ci gaba da baiwa Mata dama ta ba su kashi 35 cikin dari a manyan mukaman siyasa. Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke karbar wata kungiya mai zaman kanta da ke karfafa Mata don shiga fagen siyasa mai suna ‘Hundred Women Lobby Group’ a lokacin da suka kai masa ziyara a ofishin jam’iyyar da ke gidan Lugard.
Ya kara da cewa lokaci ya shude da Maza za su rika jagorancin mukaman da ya kamata mata su jagoranta a jam’iyyarsu ta PDP. Ya kara da cewa, PDP ta sanya Mata a bangarori daban-daban na mukamai na jagorancinta, wanda dama wannan tsari yana daga cikin kudure-kudure da tsarin mulkin PDP ya tanadar na sanya Mata a shugabanci da tsarin wakilai na jam’iyyar.
Shehu Wada Sagagi ya ce Mata suna da ‘yanci na neman yin takara na kowane irin mukami na siyasa, shi ya sa ma ake baiwa duk wacce ta fito neman takara a karkashin PDP fom kyauta.
Tun farko a jawabinta, shugabar kunkiyar ta Mata 100, Dokta Zainab Abba Gwadabe ta nemi taimakon jam’iyyar PDP wajen tabbatar da ana baiwa Mata masu inganci, ‘yan siyasa damar neman duk wani mukami ba tare da nuna bambancin jinsi ba.