Wakilinmu" />

PDP Za Ta Yi Faduwar Bakar Tasa A Gombe – Inuwa Yahaya

MUHAMMAD INUWA YAHAYA, daya ne daga cikin ‘yan takarar da suke neman kujerar gwamna a jihar Gombe, wanda ya fito neman sa’arsa a karkashin jam’iyyar APC. Inuwa ya kasance tsohon kwamishinan kudi da kuma ci gaban al’umma. A hirarsa da LEADERSHIP A Yau ya tabo batun takararsa da kuma irin gazawar da PDP ta yi a jiharsa.

 

Da wasu dalilai ne ya sanya kake neman kasancewa gwamnan Gombe?

Ina neman gwamman jihar Gombe a bisa dalilai masu tarin fa’ida da ma’ana. Ina son kasancewa gwamna ne domin na yi imanin kwarewata da kuma sanin yanayin rayuwa, shekaru da kuma iya tafiyar da mulki, sanin ilimin zamantakewa, kana da kuma sanin muhimman hanyoyin shawo kan matsalolin da suka yi wa jihar Gombe katutu. Idan ka duba irin matsanancin halin da ake ciki a yanzu, dole ne ka samu mutane da dama da suke neman kujewar gwamnan domin ceto jihar daga halin da take ciki, ba wai domin kashin kai ba. Ina da yakinin cewar ina da gagarumar rawar takawa wajen sauya jihar Gombe da kuma dawo da ita bisa turbar da ta dace ta fuskar inganta rayuwar jama’a ta hanyar hada-hadar kasuwanci da kuma shimfida nagartaccen shugabanci na gari.

 

Ta yaya kake tsammanin jam’iyyarku za ta iya kawar da PDP daga mulki?

To, akwai dai kalubalai. Amma a zahirance, idan kuka duba babban zaben da ya gudana a 2015, za ka fahimci cewar APC tana da dukkanin wasu abubuwan da ake da bukata na mallakar lashe zabe a Gombe. Mun samu kashi 75 cikin 100 na kuri’un da aka samu na shugaban kasa a jihar Gombe, sannan kuma mun samu nasarar cinye kujeru shida na ‘yan majalisu tarayya, sannan kuma mun samu nasarar cinye kujerun Sanata biyu daga cikin uku, har-ila-yau, mun kuma samu nasarar samun kujeru goma na ‘yan majalisun dokokin jiha daga cikin 24. Ko a zaben gwamnan, APC ta fadi ne don wasu dalilai. A cikin kwaryar jihar Gombe, mafiya yawan mutanen karamar hukumar Gombe sun zabe mu. Duk da ba za a rasa masu neman yin amfani da karfin iko ba, amma ina da yakin za a samu dakile hakan.

Domin a yanzu haka daga hukumomin tsaro da kuma hukumar INEC ina da yakin za a kawo karshen magudin zabe domin a baiwa jama’a damar fafata neman sa’a, kuma a bisa ilimin da jam’iyyarmu ta samu ba za mu bari a sake mana magudi a yayin zabe ba, don haka ina tabbatar maka APC za ta samu nasarar lashe shugabancin gwamna a jihar Gombe a zaben 2019 da a jiharmu. Hujja ta kuwa, ko a zaben 2015 PDP ce ta samu nasara a kujerar gwamna, amma ka ga irin nasarar da APC ta samu mana, kuma duk da irin ababen da suke jibge, balle kuma yanzu da jama’ar jihar suka gama cire tsammani daga wannan jam’iyyar, don haka amsar mulkin APC daga PDP abu ne mai sauki a wurinmu.

 

Babban taron APC na tafe a wannan makon, wane shiri kuka yi don gudanar da sahihin zaben shugabanni?

Me kake nufi da sahihi? Ba za mu fidda wani wanda bai daga cikin tsarin ba ai. A zahirance ma, wannan babban taron zaben sabbin shugabanin jam’iyyar na zuwa ne a sakamakon matsayar shugaban kasa kan hakan, kuma a ita kanta jam’iyyar ma idan ka je ka duba kundin tsarin dokokinta, tsarin mulki, idan ba haka ba mutane ba za su ci gaba ba. A takaice, matsayar da shugaban kasa ya tsaya a kai na cewar a je ga kundin tsarin dokokin jam’iyyar, a bayyana yake dole ne a koma ga filin zabe domin kada kuri’a domin samar da jagororin jam’iyyar a matakin kasa, don haka ina tabbatar maka wannan zai kawo wa jam’iyyar gagarumar nasara, domin za mu fitar da nagartaccen shugaba wanda zai kai ga a samu nasarar cin kujerar shugaban kasa, gwamnoni da sauran kujeru.

 

Wasu na cewa tuni shugaban kasa ya nuna wanda yake son ya kasance shugaban APC, me za ka ce kan wannan batun?

Ban yarda da masu yin wannan tunanin ba. Shugaban kasa yana cikin mulkin dimukradiyya ne, kuma mulkin dimukradiyya ne ya kawo shi kujerarsa a yau, don haka ba zai taba ketare dokoki da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba, don haka na sani dokar jam’iyyar ta baiwa kowa damar fita neman sa’a a kan kujeru daban-daban.

 

Shin kana ganin ‘yan Nijeriya za su yi tururuwar dangwala wa APC kuri’a a 2019?

Kwarai kuwa! APC za ta sake shugabantar Nijeriya, domin jama’ar kasar nan sun gama yanke kauna da jam’iyyar PDP a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulkin kasar nan. Nijeriya tana tafiya ne kamar kamfanoni masu zaman kasu. Allah ne ya sanya Buhari ya kasance shugaban kasar Nijeriya a karkashin inuwar APC. Domin APC tana da manufofi da kuma tsare-tsare masu kyau na ciyar da kasar nan gaba. Ko a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, ya bayyana cewar manufofinsa su ne yakar cin hanci da rashawa, matsalar tsaro, daidaita tattalin arziki kasa da kuma inganta shi. A bisa wadannan, don haka shugaban kasa mai ci ya cike dukkanin wasu muhimman abubuwan da suka dace na ya sake tsayawa maimaita shugabanci a karo na biyu, domin ya samu zarafin dorawa daga inda ya tsaya na gina kasar nan da kuma farfado da ita. Don haka ina da yakinin APC za ta sake samun gagarumar nasara a zaben da ke tafe kuma al’ummar kasar nan a shirye suke su mara mana baya domin a samu ci gaba da shimfida muhimman aiyukan da aka faro.

Kila kana maganar nan ne kawai don kai ba a Gombe kake ba, da yau za ka je ka zauna a Gombe za ka san jama’ar Gombe sun gama tsuma APC ta amshi mulki a jihar. Zan so ka je Gombe domin ganewa idonka mene ne ke faruwa a jihar, da kuma gano waye da waye suke na gaba-gaba wajen kyautata musu zaton kasancewa jagorori. Ina shaida maka cewar ko tantama ba na yi, APC za ta samu kashi sama da 70 na masu zabenta a jihar Gombe, kuma za mu amshi mulki daga hanun wadanda suka gagara kai jihar inda ta dace. Domin ita gwamnati mai ci ko na ce jagororin da suke kan mulki ba su iya gudanar da mulkin jihar ba, kila ma basu da manufofin gina jihar da jama’arta ne, don haka ne muke son mu amshi mulkin jihar domin mu gina jigar Gombe.

 

Ko za ka bayyana mana wasu kadan daga cikin shirye-shirye da kuma tsare-tsarenka wanda in ka samu nasarar cin kujerar gwamna za ka gudanar da su?

Ba zan iya jero maka su ba sakamakon yawansu, koda nan da minti goma zuwa shirin sun yi kadan na iya zayyano maka, domin ita jihar Gombe tana kunshe ne da kusan mutane miliyan 4, daga kananan hukumomi 11 da kuma jama’an da suke mabanbanta da kuma masu salo daban-daban. Gudanar da gwamnati, ya kunshi dukkanin ababen da suka shafi rayuwar jama’a ne, dukkanin hidindiminsu da suka kunshi samar musu da nagartaccen ilimi, sha’anin lafiya, ci gaban jama’a ta fuskacin aiyukan yi, inganta aiyuka, yanayin zaman takewar dan adam. Dukkanin fannonin rayuwa ina da tsare-tsare na ciyar da su gaba, domin ni manufata ta neman gwamna zai shafi kowane fanni na rayuwar jama’a na kuma yi imanin hakan.

Idan muka bisu daya bayan daya lokaci ba zai bamu ba, amma ka ga sha’anin lafiya, ilimi, harkar gona da albarkatun kasa, samar da masana’antu, habaka kasuwancin jama’a, wadannan fannonin zan fi mayar da hankalina a kansu domin idan Gombe ta kai ga samun wadannan fannonin rayuwar jama’a za ta inganta, kuma ina da tabbacin idan na zama gwamna zan yi dukkanin mai yiyuwa domin tabbatar da samuwar wadannan ababen da na ke da burin cimmawa a matsayin gwamna.

 

Har yanzu kasafin kudi na 2018 bai zama doka ba, a matsayinka na masanin kudi, mene ne ka ke tunanin ya janyo tsaikon kaddamar da kasafin?

Wannan batun na rashin mayar da kasafi don ya zama doka, ta iya iyuwa ya zama akwai siyasa ko kuma hidimar kwararru kan lamarin, amma gaskiya ni ba na son na tsunduma kaina cikin hidimar ‘yan majalisun dokoki.

Gasiya ne har yanzu jama’a suna kan muhawara dangane da kasafin nan, ko ni kaina har yanzu batun kasafin nan yana damuwa, kamata ya yi a ce ita majalisa ta bi tsarin wanda ya dace domin ganin an gudanar da abubuwa bisa gaskiya.

Amma abinda nake so jama’a su gane, a halin da ake ciki yanzu, duk da cewa Majalisa tana jan kafa wajen kaddamar da kasafin, hakan bai hana Shugaba Muhammadu buhari gudanar da ayyukan ci gaban kasa ba. Harkokin gudanarwar gwamnati suna tafiya yadda suka kamata.

 

Wane irin maki za ka iya baiwa gwamnatin Dankwambo a shekaru bakwai?

Ba na bukatar wani jinkiri wajen fadin cewar PDP ta yi matukar gazawa a jihar Gombe. Tun daga lokacin da ta dare bisa ragamar mulkin jihar na ke magana har zuwa yanzu. Bayan samun kusan naira biliyan 300 a lokuta daban-daban daga kason jihar na gwamnatin tarayya, babu inda za ka samu wani aikin da aka kammala wanda ya kai  na biliyan shida ko bakwai tsawon shekaru bakwai din Dankwambo a matsayin gwamnan jihar Gombe. Dole ne ka zakulo ababen da suke da natija da kuma wanda jama’a suke da bukata gabanin ka kawo aikin domin hakan ne zai kawo maka nasara a mulka.

Misali yanzu, babban dakin taro da ake maganar a gina, mene ne amfaninsa. A nawa tunanin, kamata ya yi a inganta harkar da tattalin arziki Gwambawa wanda hakan zai janyo hankali mutane daga wurare daban-daban. Ba ka inganta sha’anin tsaro a jihar ba, ba ka kuma samar da yanayin da zai habaka tattalin arzikin jihar ba, ta ya ya mutane za su zo.

Idan muka bar wannan, je ka ka duba tashar motoci ta kasa da kasa, wannan filin ajiye motoci na jihar Gombe ya yi kusa da kusa da babban makaranta, kwalejin ilimi ita ma tana kusa da wajen ajiye motoci na jihar Gombe, wanda hakan barazana ce ga sashi’an tsaro, ka zo wajen hada-hadar jama’a ka kawo wannan hakan ka iya kawo wa jama’a nakasu. Ina tsammanin ma jihar Gombe ba ta da bukatar irin wannan wajen ajiye motocin, kawai dai an barnata dukiya ne a banza.

Sha’anin ilimi ya fadi kasa warwas a karkashin gwamnati mai ci, domin ta yi matukar rikon sakainar ga da bangaren. Ka je ka cikin garin Gombe ka ga makarantar Firamare da Dankwanbo halarta (Ni ma na halarci wannan makarantar) nisan makarantar da gidansu bai tsawon mita 100. Babu wani abu da ya gudanar da ingantata. Sannan kuma ka tashi ka je ka ga yanayin ci gaba, babu wani ci gaba da aka samar wa jihar, kama daga fuskar walwalar jama’a, ilimi; domin idan ka bincike malaman makarantu muna matakin babu ne kawai. Idan aka ce maka ba ka samar da nagartattun malamai ba, kuma daliban ba ka kula da su ba, to ya yaya ne za kuma ka ce za a samu ci gaba? Dankwambo bai inganta malamai ba, bai kuma inganta yanayin koyo da koyarwa a jihar ba, ta yaya ne sha’anin ilimi zai je mataki na gaba?

Gwamna Goje ya yi kokarin samar da jami’a a jihar Gombe wacce ta kunshi kusan dalibai sama da 17,000, dauke da manyan sashen ilimi guda biyar. Yanzu kuma Dankwambo ya zo ya yi kaka gida kan wannan jami’ar da aka samar wa jihar Gombe. Idan muka sake waiwaiyar kwalejin ilimi ta Billiri, kwalejin kimiyya ta Bojiga, da kwalejin nazarin ilimin shari’a babu daya daga cikinsu wanda ake gudanarwa kamar yadda jama’a suke so.

Har ila yau, batun shimfida hanya da kuma gina jiha, har yanzu sama da hanyoyi 50 na unguwanin kusan 114 har yanzu babu samu hanya ba, me kake tsammanin a ce ga nasara a nan?

Kwalliya ba ta biya kudin sabulo ba a hanun gwamnati mai ci ba, domin ita PDP ba ta da manufar gina jihar Gombe, idan mu kuma muka amshi mulki za mu zakolo muhimman ababen da jama’an jihar suke so mu kuma yi musu, ba wai za mu ke yin gaba-gadi bane.

 

Wani sako kake da shi ga jagororin jam’iyyar APC dangane da karatowar babban taron jam’iyyar?

Sakona a saukake yake, kai tsaye ina kira da a maida hankali kan ainihin muhimman ababun da aka sanya a gaba domin maida hankula a kansu, kowa ya je ya dauko kundin tsarin dokokin jam’iyar da kuma bin tsarin dimukradiyya wajen tabbatar da an samar da nagartaccen shugaba kuma wanda zai ciyar da jam’iyyar gaba, wanda zai iya sanya jam’iyyar nan ta samu nasara a zaben 2019.

 

Ga jama’ar kasa dangane da karatowar lokacin zaben 2019, kana da wani sako gare su?

Shawara ta ga kowa ita ce, kar mutane su yarda da wani wanda zai yi amfani da shi wajen cimma muradinsa na kashin kai, kowa ya tsaya ya mutunta dimokradiyya domin a samu zarafin kai Nijeriya mataki na gaba.

 

A fannin samar wa matasa aikin yi, me ka tanada?

To, ina kira ga jama’a a daidaiku, gwamnatoci a dukkanin matakai, da sauran kungiyoyi, kamfanoni masu zaman kansu, da su himmatu domin samar wa matasa aiyukan yi domin samar da yanayin habaka tattalin arzikin Nijeriya. Samarwa da matasa aikin zai taimaka wajen habaka tattalin arziki.

Misali a Gombe, matasa da dama suna bukatar a samar musu da aiyukan yi amma gwamnati ta gaza kan hakan. Shi ya sa muke son idan muka samu dama za mu taba dukkanin fannonin rayuwar jama’a, matasa za su samu aiyukan yi domin dogaro da kawukansu.

 

Me kuma za ka bayyana daga karshe?

Ina fatan idan muka samu nasara a zaben 2019 mu samu nasarar gina jigar Gombe da kuma habaka tattalin arziki, ilimi, tsaro, lafiya, gona da sauran muhimman ababen da kai tsaye za su taba rayuwar talakawan jihar Gombe, fatanmu dai samun nasara ne domin muna da dumbin abubuwan da muka

Exit mobile version