Uwargidan Shugaba Xi Jinping na kasar Sin Peng Liyuan, da Sarauniya Letizia ta kasar Spain, wacce ke rakiyar Sarki Felipe na VI na Spain a ziyarar da ya kawo kasar Sin, sun ziyarci cibiyar gwaji ta kula da nakasassu ta Beijing a yau Laraba.
A cibiyar, Peng da Letizia sun saurari bayanan da aka yi kan ayyukan hidimar nakasassu kuma sun ziyarci wani babban sashen nune-nune na gasar wasannin lokacin hunturu ta nakasassu (Paralympic) ta Beijing da aka yi a shekarar 2022. Daga nan suka je zauren baje kolin kayayyakin tallafa wa nakasassu da aka kera da manyan fasahohin zamani da kuma sashen karatu na kyauta, inda suka nazarci yadda ake amfani da kayayyakin tallafa wa nakasassu, da ayyukan karatu ga yara nakasassu, da kuma tsarin samar da kayayyakin da ba su da shinge a kasar Sin.
Peng ta ce sha’anin nakasassu yana bukatar hadin gwiwa da goyon baya daga dukkan bangarori domin taimaka musu wajen shiga cikin al’umma.
Ta bayyana fatan cewa kasar Sin da Spain za su inganta mu’amala da hadin gwiwa don taimaka wa cimma burin nakasassu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














