Connect with us

RAHOTANNI

Peng Liyuan ta gabatar da jawabi kan batun shawo kan cutar tarin fuka a MDD ta bidiyo

Published

on

A Laraba 26 ga watan Satumba, an kaddamar da taron manyan wakilai kan batun shawo kan cutar tarin fuka, wato tuberculosis a Turance a lokacin da ake yin babban taron MDD karo na 73 a birnin New York na kasar Amurka, inda bisa gayyatar da aka yi mata ne, madam Peng Liyuan, wato uwargidan shugaban kasar Xi Jinping, wadda take matsayin wakiliyar kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO kan batun shawo kan cutar tarin fuka da ta Aids ta bayar da wani jawabi ta bidiyo a matsayin nagartacciyar wakiliya wajen shawo kan cutar tarin fuka.

A cikin jawabinta, Peng Liyuan da wadanda suka halarci taron sun more yadda take aiki a matsayin wakiliyar kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO kan batun shawo kan cutar tarin fuka da ta Aids tare kuma da sakamakon da fasahohin da kasar Sin ta samu cikin shekaru 10 da suka gabata wajen shawo kan cutar tarin fuka, inda madam Peng Liyuan ta bayyana yadda ma’aikatan jinya da kuma wasu mutane masu aikin sa kai suka bayar da gudummawa da kuma taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan cutar a wurare daban daban dake duk fadin kasar Sin. Peng Liyuan ta jaddada cewa, sakamakon goyon baya da kulawa daga gwamnati da kuma al’ummomin kasar Sin, tare da masu aikin sa kai kimanin dubu dari 7, kasar Sin ta samu kyakkyawan sakamako wajen shawo kan cutar tarin fuka a ‘yan shekarun nan. Wadanda suka kamu da cutar sun samu jinya da kuma sauki cikin lokaci. Yanzu aikin shawo kan cutar tarin fuka ya kasance kamar wani muhimmin abu ga gwagwarmayar yaki da talauci a wasu yankunan kasar Sin. Yawan mutanen da aka gano da suka kamu da cutar, kuma suka samu sauki ya karu a kai a kai, sannan yawan mutane wadanda suka kamu da cutar kuma suka mutu ya ragu cikin sauri. Kawo yanzu, yawan mutane wadanda suka san ilmomin shawo kan cutar ya kai fiye da 75% a duk fadin kasar Sin.

Sannan Peng Liyuan ta bayyana cewa, bisa kokarin da gwamnatocin kasa da kasa, da na kungiyoyin kasa da kasa, da na kungiyoyi da ba na gwamnati ba, da masana da kuma masu aikin sa kai, an samu muhimmin ci gaba wajen shawo kan cutar tarin fuka, amma har yanzu ana fuskantar wasu kalubaloli wajen shawo kan cutar a duk fadin duniya. An riga an zartas da “Manufar Shawo Kan Cutar Tarin Fuka” a kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO, ya kamata dukkan kasashen duniya su yi hadin gwiwa, su yi namijin kokarinsu wajen kawar da cutar tarin fuka daga duniyarmu gaba daya, domin kyautata zaman rayuwar miliyoyin mutane wadanda suka kamu da cutar.

  • Mr. María Fernanda Espinosa, shugaban babban taron MDD na wannan karo shi ne ya shugabanci bikin kaddamar da taron, inda aka zartas da “Sanarwar Siyasa Kan Batun Shawo Kan Cutar Tarin Fuka”. Amina J. Mohammed, mataimakiyar babban direktan dindindin ta MDD, da Mr. Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban direktan kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa da wasu manyan wakilan kasashen duniya sun kuma halarci taron.  (Sanusi Chen)
Advertisement

labarai