‘PEOPLE’S CONCERN FORUM’ Ta Karrama Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Katsina

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Wata kungiya mai suna People Concern Forum da ke garin Daura a jihar Katsina ta yi taron karrama danta sabon shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Sani Aliyu da wasu shuwagabanin jam’iyyar da suka samu nasara a zaban da ya gabata.

Ita wannan kungiyar kamar yadda shugabvanta Alhaji Muhammad Saled ya bayyana ya ce sun yanke shawarar karrama wadannan ‘ya ‘ya na masarautar Daura domin nuna kara da kuma karfafa masu gwiwa da kuma yi masu fatan alhaeri akan shugabanci da Allah Ya ba su.

Ya kuma kara da cewa suna sane da irin gudunmawa da wadanan mutane suka bada wajan cigaban mutanen Daura da kuma masarautar Daura wanda ya ce sun ji dadi so sai da shugabancin jam’iyyar a matakin jiha ya dawo garin su.

A jiya Lahadi ne dai ita wannan kungiya mai suna People Concern Forum ta shirya wata kasaitacciyar walima domin karrama sabon shugaban jami’yyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu Daura da sauran shugabanni da aka zaba a matakai daban-daban a jami’yyar APC ‘yan asalin masarautar Daura.

Yanzu haka dai masarautar Daura wanda take da kananan hukumomi biyar tana da manyan da kuma kananan ‘yan siyasa da suka fito daga kananan hukumomin Daura da Mai’adua da Sandamu da Baure da kuma Zango.

Wannan biki dai an gudanar da  shi ne a baban dakin taro na Daura Motel inda ‘yan uwa da abokan arziki suka yi cikar farin dango domin taya wadannan shuwagabanni na su murnar samun wannnan mukumi da Allah Ya ba su.

Da yake jawabi, kwamishinan Shari’a na jihar Katsina, Ahamd Usman el-Marzuq  ya bayyana cewa Allah da kan shi ya faɗa cikin Alqur’ani mai girma cewa shi ke ba da mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so. Babu mahalukin da Alhaji Sani JB ya je wujansa ya ce yana son shugabancin jam’iyyar APC, Allah ne ya sa zai zama shugabanta kuma ya zama.

A saboda haka ne ya yi kira ga sauran mabiya da su bada hadin kai da kuma goyan baya domin ganin wadannan shuwagabannin sun sauke nauyin da Allah ya dora masu ba tare da an samu wata matsala ba.

Shima da ya ke nasa jawabin sabon Shugaban Jami’yyar APC na Jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu Daura ya bayyana jin dadinsa bisa ga wannan karamci ya kuma sha alwashin in Allah Ya yarda ba zan bada kunya ba.

“Yanzu baban abinda muke bukata daga wajanku ‘yan uwan shi ne a ci gaba da yi mana addu’ar samun ganin mun samu nasara ta wannan mulki da mu ka samu, don ganin mun sauke wannan nauyi da al’ummar jihar Katsina suka dora mana, da yardar Allah ba za mu ba ku kunya ba. “ inji shi

Sani JB ya bada tabbacin cewa idan ya samu hadin kai da yake bukuta lallai zai kwantata adalci a wannan tafiya ta su, kuma za su yi iyakar kokarinsu wajan ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zabe mai zuwa na 2023.

Daga karshe ya yi wani kira na musamman  ga al’ummar jihar Katsina da su maida hankali wajen yin katin zabe da hukumar zabe mai zaman Kanta take shirin farawa a matakin gundumomi.

Daga cikin wadanda sula halarci wannan taro akwai wakilin Sakataran gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muammad Inuwa da kakakin Majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Tasi’u Maigari da kwamishin kananan hukumomi da masarautu, Hon. Ya’u Umar Gwajo-gwajo da masu taimakawa gwamna akan bangarori daban-daban da ‘yan majalisar jiha da ‘yan uwa da abokan arziki

Exit mobile version