Perisic Yafi Son Koma Wa Tottenham A Kan Arsenal

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan, Iban Perisic yafi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham akan Arsenla saboda kwallonsa zatafi dacewa da Tottenham.
Perisic, wanda a shekarar data tabata aka dinga dangan tashi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a watan daya gabata na Janairu yakusa komawa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a matsayin aro sai dai daga baya kungiyar sa tace ba za ta bayar da aronsa ba sai dai a siya.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai ta kusa kammala cinikinsa sai dai cinikin ya rushe bayan da kungiyar ta kori kociyanta Jose Mourinho wanda daman shine yake son siyan dan wasan.
A kwanakin baya mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery ya bayyana cewa sunso siyan Perisic sai dai aro suka so a basu zuwa karshen kakar wasa inda zasu biya kudinsa idan kungiyar ta fitar da kudin siyan ‘yan wasa.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Perisic, mai shekara 30 a duniya yafi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham saboda yana ganin kungiyar tana shiga cikin hudun farko na gasar firimiya a duk shekara.
Acikin watan Janairun daya gabata ne dai Perisic ya roki kungiyar ta Inter Millan ta siyar dashi zuwa kasar Ingila sai dai kungiyar bata samu kungiyar data nuna tanason yin cinikin dan wasan ba amma a kakar wasa mai zuwa zata siyar da dan wasan wanda aka yiwa kudi fam miliyan 35.

Exit mobile version