Petrove: Mutumin Da Ya Hana Duniya Tarwatsewa Ya Rasu

Daga El-Zaharadeen Umar

Stanislab Yebgrafovich Petrov ya kasance laftanar-kanal ne a ma’aikatar tsaro ta sobient wanda aka fi sani da mutumin da shi ka dai ya ceci duniya daga tarwatsewar harin makami mai linzami saboda irin rawar da ya taka a shekarar 1983 na kin bada labarin gaskiya game da harin makami mai linzami

A ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 1983, sati uka bayan da sojojin Tarayyar Sobiyat suka kakkabo jirgin yakin kasar Koriya, mai lamba 007. Petrob a lokacin yana babban jami’in soja mai kula tashar makamin Nukiliya, aka bada rahotan cewa Kasar Amurka ta yi amfani da makami mai linzami a kasar ta Rasha

Sai dai kuma Petrov bai amince da wannan rahota  ba a matsayin na gaskiya ba wanda haka ya yi sanadiyar kin maida martanin makamin Nukiliya ga Kasar Amurka wanda a karshe kungiyar NATO ta daidai al’amarin makami mai linzami. Kazalika bincike ya tabbatar da cewa tauraron dan adam na Sobiet ya samu matsala a wancen lokacin.

Shi dai Petrov an haife shi ne a ranar 7 ga watan satumba a shekarar 1939 a garin Bladibostok mahaifinsa kuma ya yi batan dabo a lokacin yakin duniya na biyu. Sannan an  sa shi Babbar makarantar koyan aikin injiniya ta mayakan sojojin sama, bayan da ya kamala ne ya shiga aikin a ma’aikatar tsaro ta Sobient.

A shekarar 1970 aka nada Petrov a matsayin mai kula wani sabon sansanin dakile hare-haren Makamai masu linzami daga kasashen da ke cikin kungiyar NATO. Haka kuma yana da mata mai suna Raisa tare da namiji mai suna Dimitri da kuma mace Yelena.

Kamar yadda Babbar jami’in tarayya Rasha ya bayyana a ranar 19 ga watan janairun 2016, bayan kwashe kimanin shekaru 22 da faruwar wancan hadarin, ya ce sun tabbatar da wancan rahotan kai harin makami mai linzami, bayan da ta bayyana cewa wancan hadari ya afku, sai Petrob ya fada da bakinsa cewa yanzu ko dai a yi masa sakayya ko kuma a hukunta shi.

Haka kuma ya kara da cewa rahotan da suka samu na cewa akwai wasu hare-hare daga Kasar Amurka wanda su ka haddasa wancan na farko ya tabbatar da cewa na’ura mai kwakwa da suke amfani da ita ta ba su bayyanan bogi. Ya ce sai daga baya suka gane cewa yana da gaskiya babu wata barazana da ta kusance na’urar kwanfutar su da suke amfani da ita, kawai dai an kirkira labarai kanzon kurege ne domin cimma wata manufa, sannan daga baya baya suka fahimce cewa dalilin kirkirar wancan batu shi ne domin a dadadawa yankin Dakota ta arewa da wani bangare na Molniya amma daga baya an gyara komi ya tafi dai dai.

Daga baya kuma Petrov ya nuna cewa bukatuwar da ke akwai na ya bada ta shi matsayar wanda daga baya ya sanar da matukan kasar Amurka cewa makamai masu guba biyar ne aka yi amfani da su, kuma aka yi masu kuste a na’ura mai kwakwalwa, a na shi bangaran wannan bai zama wani abu da zai sa ya kariya ba duk cewa sai daga baya ya samu babar hujja.

A shekarar 2013 a wata hira da aka yi da Petrob ya bayyana cewa a wancan lokacin bai taba tsammanin abubuwan da aka fada kuskure ba ne, ya ce bai yi zaton wani farar hula zai iya fadin abinda soja wanda aka bashi hore tare da bin dokoki ya kasa fada ba.

Petrob ya sha tambayoyi daga manyansa akan hukuncin da ya dauka, saboda kawai ya tsaya kyam akan abinda ya sa gaba. Wani babban janaral mai suna Yury Botintseb wanda kuma babban kwamanda ne a bangaran makami mai linzami a tarayyar Sobient, wanda shi ya fara jin rahotan Petrob akan wancan hadari, ya ce gyara kuskuran da Petrob ya zama babban abin lura anan gaba. Petrov da kansa ya fada inda ya ce janaral Botintseb ya yi masa alkawarin sakayya amma sai ya tuna da cewa shi fa babban Malami ne da yake aikin bisa cancanta saboda haka ba zai bayyana wannan hadari ackin kudin tarihin yaki ba.

Bai karbi wata sakayya ba saboda yadda wannan hadari ya zama wani abin ban kunya ga wadanda suke hura hanci, tare da fadin cewa suna ilimin kimiya sai gashi su suka zama sanadin faruwar hakan. An sake tura shi zuwa wani karamin sansani inda daga karshe ya ajiye aikin wanda ya ce ba tursasashi aka yi ba, shi a kashin kansa ya ajiye.

A wata zantawar da ya yi da manema labaria mista Petrob ya ce sanan nan jan kwala sojojin nan ba zai taba aiki ba, a kwakwalwa sojoji saboda haka ba za a taba dauka matsaya ba akan wani batu na yaki ba, a hannu wani mutun kwara daya ba. Lokacin da wannan hadari ya bayyana a idon duniya ta kafar sadarwa a shekarar 1990 ya kara wayar da kan jama’a game da wancan batu na daukar matsayar da mista Petrob ya yi.

Akwai rikitarwa game da abinda mista Petrov ya yi acikin aikin soja, a lokacin wancan hatsarin, a matsayinsa na mutun guda bashi da damar daukar wani mataki na maida martani akan harin makami mai linzamai, babban aikinsa a lokacin shi ne, ya rika lura da na’ura mai sarrafa kanta da kuma kayan aikin, sannan ya rika bada rahotan duk wani yunkuri  na kai hari. Manyan jami’an sojan sobient ne kadai ke da ikon bada umarnin a maida martani akan duk ya kawo hari.

Mista Petrov ya kara bayyana cewa bai taba tsammanin cewa zai fuskanci irin wannan yanayin da ya shiga ba. ‘’A iya sani na, ni ne  mutun na farko da na taba shiga irin wannan halin, wannan ne zai zama na karshe da zai sake faruwa inda ba bisa tsautsayi ba’’. In ji shi.

Bayan wani dogon lokaci tarayyar Sobient ta gudanar da wani bincike akan wancan al’amari inda ta dauki matsaya cewa Petrob baya da gamsashen hujja akan abinda ya yi lokacin rigima. Saboda yana da wayar salula a hannu daya sannan yana yin tarho da hannun guda, to baya da wani hannu da zai iya wani amfani da shi.

A shekarar 1964, Petrob ya ajiye aikin soja inda ya samu wani aikin a wata hukumar bincike da cigaban tarayyar Sobient ta samar, amma daga baya kuma ya yi ritaya bayan da matarsa ta kamu da cutar ciwon kansa, saboda ya kula da ita a gida.

Mista Petrob dai ya koma ga mahaliccinsa a ranar 19 ga watan Mayu 2017,  a sakamako kamuwa da wata cuta wanda kuma ba a bayyanawa duniya rasuwarsa ba sai a watan satumba 2017.

A ranar 21 ga watan Mayu 2004, wata kungiya mai suna ‘’The San Francisco-based Association’’ ta shirya wani babban gangami domin karama Petrov da kudi har dalar Amurka 1000 saboda muhimmiyar rawar da ya take na kin tarwatsa duniya.

Haka kuma a watan Janairun shekarar 2006, petrob ya yi wata tafiya zuwa kasar Amurka inda nan ma aka karrama shi a birnin New York. Haka kuma  ita wannan kungiyar mai suna ‘’The San Francisco-based Association’’ a matsayin  cikakken dan kasa nagari.

Akan matakin da Petrov ya dauka na tseratar da duniya daga harin makami mai linzami a lokacin yaki a shekarar 1983, ya bashi damar samun wasu kyautuka da kuma girmamawa daga bangarori da dama da suka hada da kudadan Yuro da dalar Amurka masu tarin yawa, sannan ya samu wata karramawa daga bangaran kafar yada labarai a kasar Jamus.

‘’Kafin tabbatar da faruwar lamarin irin wannan dole a zurfafa bincike na gaskiya da gaskiya ta hanyar bayanan sirri da kuma rahotannin jami’an tsaron na sirin.’  in ji wani jami’I mai suna Bruce Blair.

Petrov ya ce bai taba tunani wata rana za a rika ganinsa a matsayin wani jarumi ba, saboda abinda ya yi a wancan lokaci. A wata hira da aka yi da shi wanda kuma aka haska a wani Fim mai suna ‘’Mutumin da ya ceci duniya’’ ya kara da cewa duk abubuwan da suka faru da shi a dalilin aikinsa ne, ‘’saboda kawai ina aikina ne, haka ta faru da ni, ni mutun ne mai saukin kai a kowane lokaci, matata wadda ta rasu shekaru goma da suka wuce ba ta san wannan labarin ba’’ in ji mista Petrob.

 

Exit mobile version