Daga Abba Ibrahim Wada
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon ɗan wasan Manchester united da Everton Phil Neɓille na son karbar aikin koyarda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton.
Kulob din Everton ya kori Ronald Koeman ranar Litinin bayan da Arsenal ta doke su a gasar Firimiya.
Rashin nasarar ya jefa ƙungiyar sahun kulob uku da ka iya faduwa a gasar idan suka ƙare a haka.
A baya ya taba zamowa mataimakin koci a ƙungiyar Ɓalencia ta La Ligar kasar Spaniya lokacin da ƙungiyar ta Ɓalencia ta dauki ɗan uwansa, Gary Naville.
A ranar Talata ne Everton ta tabbatar da cewa kocin tawagar ‘yan kasa da shekara 23 Daɓid Unsworth zai ci gaba da jan ragamar kulob din a matsayin riko.
Zai kuma fara jan ragamar kulob din a wasan da za su yi ranar Laraba a gasar cin kofin Carabao da Chelsea.