Abba Ibrahim Wada" />

Pochettino Ne Zai Maye Gurbin Mourinho

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ed Wood ward yafi son ganin mai koyar da kungiyar Tottenham, Mauricio Pochettino ya maye gurbin Mourinho idan har kungiyar ta sallameshi.

Kwanakin Mourinho dai a Manchester United suna neman karewa bayan da kungiyar bata fara buga kakar wasa cikin nasara ba inda rabon da kungiyar tasha wahala a wasannin farko a kakar wasa  yau kusan shekara 30 kenan.

Hakan yasa aka fara rade radin cewa Mourinho zai iya rasa aikinsa idan har abubuwa basu koma yadda suke ba kamar baya kuma tuni aka fara tunanin wanda zai maye gurbin kociyan dan kasar Portugal

Sai dai tuni daman aka fara danganta tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane domin ya maye gurbin na Mourinho sai dai wasu rahotanni sunce babu tabbas wancan zargi da akeyi.

Idan har Mourinho bai samu damar samun nasara a wasan yau ba da kungiyar zata buga da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle zai iya rasa aikinsa domin wasa biyar kenan kungiyar bata samu nasara ba.

Duk da cewa Zidane yanzu baya koyar da kowacce kungiya kuma zaifi saukin samu amma an bayyana cewa shugaban kungiyar yafi tunanin daukar Pochettino daga Tottenham

Sai dai kungiyar Tottenham zatayi iya yinta wajen ganin ta hana mai koyarwar tafiya musamman ma da a kwanakin baya ya sake sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta tsawon shekaru biyar.

Exit mobile version