Kocin kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain Mauricio Pochettino ya kamu da cutar korona kuma hakan na nufin ba zai jagoranci fafatawa biyu da kungiyar za ta yi ba a nan gaba kamar yadda kungiyar ta bayyana.
A makon nan ne a karon farko tsohon kocin na Tottenham, mai shekara 48 a duniya, ya lashe kofi a tarihi tun bayan da ya fara aikin horas da kwallon kafa bayan da a ranar Laraba, Paris St Germain ta doke Marseille da ci 2-1 ta lashe Fench Super Cup da ake kira Trophee des Champions.
PGS ta fafata da kungiyar Angers a ranar Asabar a gasar Ligue 1 sannan za ta kara da kungiyar kwallon kafa ta Montpellier ranar Juma’a, 22 ga watan Janairu kuma duka an tabbatar da cewa Pochettino ba zai halarci wasanninba.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce gwajin da aka yi kan Pochettino ya nuna cewa yana dauke da cutar Cobid-19 saboda haka zai killace kansa na tswon lokacin da likitoci suka bukata kafin a sake gwada shi.
PSG, wadda ta lashe kofi takwas na gasar Ligue 1 a baya, ita ce ta biyu a saman teburin gasar bayan ta fafata a wasanni 19, inda take bayan Lyon da tazarar maki daya kuma nasarar da suka yi a kan Marseille ranar Laraba ita ce karon farko da Pochettino ya lashe kofi a tarihinsa na horar da ‘yan wasan kwallon kafa.
Tsohon dan wasan na Espanyol da Argentina, wanda kuma ya kwashe shekara biyu yana buga wasa a PSG a matsayin dan wasa, ya taba jagorantar kungiyar Espanyol, Southampton ta kuma Totttenham kafin ya maye gurbin Thomas Tuchel a PSG.