Daga Abba Ibrahim Wada
Ɗan wasan Manchester United Paul Pogba na gab da dawowa filin wasa, duk da dai kocin Ƙungiyar Jose Mourinho bai ba da cikaken tabbacin yaushe Pogba zai koma taka leda ba.
United ta soma wannan kakar da Ƙarfinta, kafin Pogba ya ji rauni a karawarta da Basel a watan da ya gabata.
United ce ta biyu a teburin Firimiya, kuma ta na shirin karawar da Huddersfild Town a yau Asabar.