Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa dan wasa Paul Pogba yana cikin farin ciki a kungiyar kuma zai bawa duniya mamaki daga yanzu har zuwa karshen kakar wasa ta bana.
A kwanakin baya ne wakilin dan wasa Pogba kuma mai kula da harkokin wasanninsa, Mino Rioala ya bayyana cewa Pogba baya jin dadin wasa a Manchester United ya kamata ya sauya kungiya a watan Janairu
A watan Yunin shekara ta 2022 kwantiragin dan wasan tawagar Faransa zai kare, zai kuma iya barin Old Trafford a watan Janairun shekara ta 2022 a matakin wanda bai da yarjejeniya kuma Pogba mai shekara 27, ya buga wasanni goma a gasar Premier League har da shida da aka fara bugawa da shi a fili a kakar bana.
Sai dai tuni aka fara danganta dan wasan Faransa da kungiyoyi daban daban wadanda suka nemeshi a kwanakin baya kamar Real Madrid da Juventus da kuma kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta kasar Faransa.
Amma Pogba, wanda ya sake komawa Manchester United daga Juventus a shekarar 2016, bai boye aniyarsa ta buga wasa a Real Madrid nan gaba ba kuma a watan Nuwamban daya gabata kocin tawagar Faransa, Didier Deschamps ya sanar cewa ”Pogba ba zai taba samun farinciki a United a irin halin da ya tsinci kanshi ba.”
Wasanni 22 Pogba ya buga a dukkan fafatawa a bara a Manchester United, sakamakon raunin da ya yi ta jinya, amma a watan Agusta Raiola ya ce za su zauna don tsawaita kwantiragin dan kwallon sai dai za’a iya cewa yanzu yayi amai ya lashe