Abba Ibrahim Wada" />

Pogba Na Son Barin United A Watan Janairu

Jaridun Birtaniya sun rawaito cewa, dan wasan Faransa da ya nuna bajintarsa a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Rasha, wato Paul Pogba ya tsayar da shawarar kawo karshen tankiyar da ke tsakaninsa da kocin kungiyarsa ta Manchester United, Jose Mourinho, in da zai koma Barcelona da murza leda a watan Janairu.

Pogba wanda ya zura kwallo a wasan karshe da Faransa ta doke Croatia da ci 4-2 a gasar ta cin kofin duniyar, ya amince da kulla kwantiragi da Barcelona akan farashin fam miliyan 89.5, kwatankwacin Dala miliyan 115.

An ruwaito cewa, Pogba zai kulla kwantiragin ne na tsawon shekaru biyar, in da zai rika karbar albashin Pam dubu 346 a kowanne mako, kwatankwacin Nairar Najeriya, miliyan 16 da doriya, kudin da ya kusan ninka albashinsa a Manchester United.

Jaridu Sun ta rawaito cewa, Pogba ya bukaci Manchester United data kara masa albashinsa a kowanne mako daga Pam dubu 180 zuwa Pam dubu 380 ko kuma ya raba gari da ita.

Sai dai ana ganin mawuyaci ne Manchester United ta sayar da Pogba wanda ta sayo daga Jubentus akan Pam miliyan 89 a shekarar 2016 daga Jubentus.

Exit mobile version