Pogba Shi Ya Janyo Wa Kansa Rauni – Mourinho

Rahotanni sun bayyana cewa mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya zargi dan wasansa Paul Pogba sakamakon ciwon da ya samu, inda ya ce Pogba yana amfani da wani mutum daban da yake bashi horo, sannan kuma ba ya daukar shawarar da likitocin kungiyar suke bashi.

Ranar Talata ne ya yi raunin a wasan cin kofin zakarun Turai da suka kara da Basel, inda suka yi nasar da ci 3-0. Dalilin wannan ciwo da ya ji, Pogba zai yi jinyar mako shida.

Pogba ba zai buga wasan da United za ta kara da Eberton da Southampton da kuma Crystal Palace ba. Kuma ba zai yi wasan zagaye na uku da za su yi ranar larabar makon gobe da Burton ba, da kuma wasan gasar zakarun turai da za su je CSKA Moscow ranar 27 ga watan nan.

Haka kuma ba zai shiga wasan neman shiga gasar kofin duniya ta Faransa da za su kara da Bulgaria da Belarus a farkon watan Oktoba ba, wacce suke fatan samun nasara don tabbatar da gurbinsu a Rasha kaka mai zuwa.

Exit mobile version