Abba Ibrahim Wada" />

Pogba Yana Son Komawa Jubentus Saboda Ronaldo

Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba ya bayyana cewa yanason barin kungiyar Manchester United zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Jubentus saboda bayason zama da Mourinho.

Mourinho ya koma Manchester United shekaru biyu da suka gabata sai dai tun bayan komawarsa kungiyar baya buga abinda akayi zaton zai buga wanda hakan yaja masa suka ciki daga wajen kasar Ingila ciki har da Jose Mourinho.

Pogba dai ya buga gasar cin kofin duniya inda yayi abin azo agani a gasar bayan ya taimakawa kasar Faransa ta lashe gasar sai dai nan gaba kadan zai koma kungiyarsa bayan ya kammala hutun da aka bashi bayan kammala kofin duniya.

Pogba dai yanason yaci gaba da buga wasa irin wanda yabuga a gasar cin kofin duniya sai dai bayason cigaba da buga wasa a Manchester United saboda yana ganin bazai samu cigaba da wasansa ba.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa shima wakilin dan wasan Mino Riola ya sanar da shugabannin Manchester United cewa dan wasan yanason barin kungiyar domin zuwa inda zai dinga samun farin ciki idan yana buga wasa.

Pogba dai ya taso a karamar kungiyar Manchester United tun yana matashin dan wasa kafin kuma yakoma kungiyar Jubentus a karkashin tsohon mai kai koyarwa Sir Aled Ferguson.

 

Exit mobile version