Watakila dan wasan Manchester United Paul Pogba zai ci gaba da buga wasa a kungiyar, domin da kyar a kammala cinikinsa a cikin watan Janairu in ji wakilinsa a fannin kwallon kafa kuma mai kula da harkokin wasannin dan wasan..
A baya can Mino Raiola ya ce dan kwallon tawagar Faransan mai shekara 27 baya jin dadin buga wasa a Old Trafford, ya kamata ya sauya kungiya sai dai Pogba ya bayyana irin kwazon da zai ci gaba da sawa a kungiyar, bayan da aka dunga caccakar kalaman wakilin nasa.
Raiola ya taba sanar da cewar Pogba na son barin Manchester United da zarar an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo, amma ya kara da cewar yana magana kan kasuwar badi kenan wadda za’a bude nan gaba.
”Da wuya kaga manyan kungiyoyi na cinikayyar fitattun ‘yan wasa a watan Janairu amma bari muga abinda zai faru bayan kammala kakar bana domin bayan kammala kakar wasa ne kowacce kungiya take sake sabon shiri” in ji wakilin na Pogba
Dan kasar Faransan ya ci kwallo 35 a wasa 172, sai dai United ta kasa lashe kofi tun shekarar 2016 zuwa 2017 lokacin da ta dauki gasar EFL da kuma Europa League a lokacin tsohon kociyan kungiyar Jose Mourinho.
Pogba ya buga wasanni shida da aka fara da shi daga 11 da ya yi a Premier League ta bana da cin kwallo biyu, ya kuma yi sanadin fenareti biyu da aka ci Manchester United duka a wannan kakar da ake bugawa ta bana.