Portugal Ta Lashe Kofin ‘UEFA Nations League’

Kasar Portugal ta zama kasa ta farko da ta lashe kofin ‘UEFA Nations League’ bayan da dan wasan kasar Goncalo Guedes ya zura kwallon daya mai ban haushi da ya ba su damar doke kasar Holland a wasan karshe da aka buga a daren Lahadi.

Guedes, mai shekara 22, ya samu nasarar zura kwallon bayan da dan wasa Bernando Silva ya ba shi kwallon, inda ya yi wa kwallon duka mai karfi wanda mai tsaron gidan Holland din Jasper Cillessen ya kasa rike kwallon ta shige raga.

Baya ga kofin nahiyar Turai da suka lashe akan Faransa a shekarar 2016, yanzu ma sun kara lashe wani kofin a hannun Holland.

Kwallaye Uku da Christiano Ronaldo ya zura a ragar kasar Switzerland a ranar Laraba, shi ya bai wa Portugal damar zuwa buga wasan karshe.

Exit mobile version