Khalid Idris Doya" />

PRP Ta Taimaka Wa Matar Malam Aminu Kano

Shugabanni da mambobin jam’iyyar ‘People’s Redemption Party’ (PRP) reshen jihar Bauchi, a ranar Litinin ne suka ziyarci matar jarumin da ya jagoranci assasa jam’iyyarsu, Malam Aminu Kano domin taimaka wa rayuwarta da na iyalan marigayin.
A lokacin ziyarar, tawagar jam’iyyar sun mika mata kyautar kayyakin masarufi da kuma kudade a gidanta da ke unguwar Allura a karamar hukumar Bauchi.
Shugaban jam’iyyar a jihar Bauchi, Alhaji Shehu Barau Ningi, wanda ya jagoranci shugabannin jam’iyyar zuwa kai ziyara wa Hajiya Asma’u Amina Kano, ya shaida cewar ziyarar sun yi ne domin ta sansu, su san juna da kuma neman albarkanta a matsayinta ma matar wanda ya kafa jam’iyyar.
A cewarshi, lura da jarumtar mijinta wajen kafa jam’iyyar mai kyawawa manufofi da kuma kasancewarsa jigo tauraro a siyasar kasar nan, da bukatar su zo domin su kawo mata ziyara ta musamman.
Kamar yadda yake cewa, jarumin mijin nata, ba za su taba iya mance gudunmawa da rawar da ya taka wajen ci gaban siyasar kasar nan ba.
“Marigayi Malam Aminu Kano, masani ne kan harkokin siyasa, jarumi mai tabbatar da kyautata zaman lafiya, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa waje ci gaban kasa ba za mu taba mancewa da kokarinsa ba. A bisa haka ne, muka kawo miki ziyara mu gaisheki a matsayinki na uwa a garemu,” A cewar shi.
Da take maida jawabin godiya, Hajiya Asma’u Aminu Kano, ta nuna godiyarta a bisa ziyarar da jam’iyyar ta kawo mata, tana mai bayanin cewar tabbas sun karramata.
Ta bukacesu da su kasance masu biyayya a hidimar siyasa, ta na mai cewa marigayi mijinta wanda shine ya assasa jam’iyar PRP, ya tabbatar da aiwatar da biyayya da ladabi a cikin jam’iyyar wanda a cewarta sam koda wasa bai amincewa da gurguwar fahimta daga magoya baya ko mambobin jam’iyyar, ta ce ya yi amfani da damarsa wajen gina jam’iyya mai cike da tsari.
“Ya na kula sosai da jin dadin al’umma da mutanen jam’iyyarsa fiye da tasa. Ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban kasar nan,” a cewarta.

Exit mobile version