‘PSG Ba Ta Da Niyyar Sallamar Pochettino’

PSG

Dan jaridar da ke bayar da labarai kan kwallon kafa musamman labaran da suka shafi kasashen Faransa da Sipaniya, Guillem Balague ya ce Paris St-Germain ba ta da niyyar barin kocinta Mauricio Pochettino ya bar kungiyar.

Tottenham dai ta tuntubi kocin mai shekara 49 game da yiwuwar komawa kungiyar da koyarwa, inda ya kwashe shekara biyar yana aiki kafin kungiyar ta sallame shi a kakar data gabata.

Kungioyar tana son sake Daukar Pochettino ne bayan da aka samun ingantuwar dangantaka da mamallakin Kungiyar, Daniel Leby, wanda tun farko alakarsu ta lalace da Pochettino saboda rashin nasarar da kungiyar ta fuskanta a baya.

“Pochettino yana fatan komawa Ingila, amma tuni ya soma shirin kakar wasa mai zuwa da masu ruwa da tsaki na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German wadda take neman lashe gasar Lig 1,” in ji Balague.

Ya ci gaba da cewa “PSG ba ta da niyyar barinsa ya tafi kuma ta yi mamaki kan yadda ake cewa za ta sallame shi domin kuwa babu kanshin gaskiya a cikin labaran da ake yadawa akan kociyan, dan Argentina.”

Balague ya ce annobar korona  da matsalolin da ta haddasa na hana tafiye-tafiye – ta sa rayuwa ta yi wa dan Argentina wahala a Paris, domin kuwa rabin iyalansa suna zaune a London.

Tottenham ta kori Jose Mourinho, kocin da ya maye gurbin Pochettino, a watan jiya kuma tana nazari kan yadda za ta samu wanda zai zama sabon koci domin tunkarar kakar wasa mai zuwa.

Kocin makarantar horas da ‘yan wasan kungiyar, Ryan Mason shine yanzu yake rikon kwarya zuwa karshen kakar wasan bana a karkashin jagorancinsa, Tottenham ta sha kashi a hannun Manchester City a wasan karshe na Carabao Cup kuma ta kare a mataki na bakwai a gasar Firimiya ta Ingila ta kakar.

Exit mobile version