Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Leandro Paredes, ya ce kungiyarsa ta soma shirye-shiryen kulla yarjejeniya da kaftin din Barcelona Lionel Messi, mai rike da kambun gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya guda 6 domin ganin ya koma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
A karshen kakar wasa ta bana ne dai yarjejeniyar Messi da Barcelona za ta kare, bayan kokarin katse ta da dan wasan yayi a shekarar bara, abinda ya janyo kai ruwa rana tsakaninsa da kungiyar wanda har sai da shugaban gudanarwar kungiyar Jose Maria Bartemeu yayi murabus daga kujerarsa sakamakon matsin lamba.
Tun kakar wasa ta bara ne kuma ake alakanta Messi da komawa PSG ko kuma Manchester City, kungiyar da a waccan lokacin har ta tattauna da maihafin tauraron dan wasan domin ganin ta kulla yarjejeniya dashi.
Kwallaye 14 Messi ya ci wa Barcelona a dukkanin wasannin da ya buga mata a kakar wasa ta bana wanda hakan yasa ake ganin har yanzu zai bada gudunmawa a duk inda yaje sai dai a wannan satin bai buga wasan da Barcelona ta samu nasara ba daci 2-0 akan kungiyar Elche ba sakamakon dakatarwar da akayi masa ta wasanni biyu.