Babbar kungiyar kwallon kafa ta Faransa Paris St Germain PSG ta kori kociyanta haifaffen kasar jamus, Thomas Tuchel.
Jaridar wasanni ta Faransa L’Equipe da jaridar Bild ta Jamus suka bada rahoton korar a yau Alhamis.
Amma dai har yanzu kungiyar bata yi magana game da rahoton ba.
Tuchel, wanda ya jagoranci PSG zuwa wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai a watan Agusta wanda suka sha kashi a hannun Bayern Munich, ya jagoranci wasan da suka doke kungiyar Racing Strasbourg da ci 4-0 kasa da sa’o’i 24 da suka gabata.
An nada Thomas Tuchel dan shekaru 47 a matsayin mai horar da PSG a shekarar 2018 kuma ya lashe kofunan Ligue 1 biyu.
Duk da cewa PSG ba ta jagorantar Ligue 1 a wannan karon kamar yadda ta saba a shekarun baya, Tuchel ya jagorance ta zuwa gasar zakarun Turai zagaye na 16 inda za ta kara da Barcelona.
Wannan ya kasance bayan sun gama a saman rukuni wanda ya hada da RB Leipzig Manchester United da Istanbul Basaksehir.