Dan kasar Argentina mai shekara 48, ya maye gurbin Thomas Tuchel, kuma ya sanya hannu kan kwantaragi har zuwa 30 ga watan Yunin 2022, tare da zabin kara tsawaita kwantaragin ta sa na shekara daya.
Pochettino wanda ya bugawa PSG kwallo tsakanin 2001 zuwa 2003, baya da kungiyar da yake jagoranta tun bayan korarsa da Tottenham ta yi a watan Nuwambar 2019.
PSG dai ita ce ta uku a jadawalin gasar Ligue 1 ta faransa, kuma za ta buga wasanta na gasar zakarun Turai a watan Fabrairu da Barcelona a zagayen 16.