Abba Ibrahimm Wada" />

PSG Tana Jiran Amsar Cigaba Da Zama Ko Tafiya Daga Mbappe

Mbappe

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German tana jiran amsa daga dan wasanta, Kylian Mbappe, wanda a kwanakin baya ya bayyana cewa bai yanke hukuncin kungiyar da zai bugawa wasa ba a kakar wasa mai zuwa.

A kwanakin baya kungiyar ta PSG ta soma tuntubar dan wasan Kylian Mbappe a kan bukatar sabunta yarjejeniyarsu dake shirin karewa a shekara ta 2022 duk da cewa har yanzu babu wata Magana mai kwari da aka tattauna.
A baya bayan nan ne dai Mbappe ya bayyana cewa har yanzu bai yanke shawarar ci gaba da zama a PSG ba, ko kuma ya sauya sheka zuwa wata kungiyar, wadda ake kyautata zaton ba za ta wuce Real Madrid ba.
A ranar Lahadi ne dan wasan kungiyar Neymar ya tabbatar da cewa zai ci gaba da zaman kungiyar kum yayi kira da dan wasa Mbappe akan ya amince shima ya ci gaba da zaman kungiyar ta kasar Faransa.
Sai dai a bangaren Real Madrid da ta jima tana bibiyar bajintar dan wasan, zai yi wahala ta iya kulla yarjejeniya da shi a nan kusa, la’akari da kalubale har kashi biyu dake gabanta wanda tana bukatar maganace su.
kalubale na farko dai shi ne raguwar kudaden shigar da take samu saboda annobar Korona, sai kuma bashin yuro miliyan 570 da ta karba domin sake fasalin filin wasanta na Santiago Bernabeu, wanda za ta fara biya a farkon shekarar 2022, kuma kawo yanzu yuro miliyan 100 ya zo hannun kungiyar, yayin da ragowar kuma sai watan Yunin shekarar ta 2022.
Kawo yanzu dai Mbappe na karbar albashin yuro miliyan 21 ne duk shekara a PSG wanda ake ganin a halin da ake ciki babu wani dan wasa da yake karbar albashin da dan wasan yake karba tun bayan da kungiyar ta bayar da aron dan wasa Gareth Bale

Exit mobile version