Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain, Mauricio Pochettino, ya yi nasara a karon farko a wasan da ya ja ragamar kungiyar ta doke kungiyar Brest da ci 3-0 a gasa Likue 1 ta kasar Faransa.
Dan wasan gaba na kungiyar, Moise Kean dan wasan tawagar Faransa shi ne ya fara ci wa PSG kwallon farko, kawo yanzu ya zura tara a raga a wasa 14 da ya buga a gasar Faransa kuma yana zaman aro ne daga kungiyar Everton.
Sai dan kasar Argentina, Mauro Icardi wanda ya kara kwallo ta biyu, sannan Pablo Sarabia ya ci ta uku tun daga yadi na 20 wanda sakamakon hakan ya bawa PSG nasarar farko tun bayan fara aikinsa da kungiyar.
Da wannan sakamakon kawo yanzu sauran maki daya ya rage tsakanin PSG ta biyu a teburi da mai jan ragamar gasar ta kasar Faransa Lyon wadda ta buga 2-2 a gidan kungiyar kwallon kafa ta Rennes
PSG, ta buga karawar ba tare da dan kwallon Brazil ba, Neymar, wanda ke jinya sai dai duk da haka kungiyar ta samu nasara da gagarumin rinjaye sannan a ranar Asabar Paris Dt Grmain za ta ziyarci Angers, ita kuwa Lyon za ta karbi bakuncin FC Metz a gasar ta Ligue 1.