PSG Za Ta Taya De Bruyn Na Manchester City

Daga Abba Ibrahim Wada

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG ta ƙasar faransa ta bayyana aniyarta na taya ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Manchester city, keɓin De Bruyn domin yakoma ƙungiyar ta PSG.

Ɗan wasan ɗan shekara 25 a duniya, yaja hankalin ƙungiyoyi tun lokacin da yake taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wolsburg dake ƙasar jamus inda Manchester city din ce tasamu nasarar daukar ɗan wasan.

Sai a halin yanzu PSG ta bayyana aniyarta na sake neman ɗan wasan inda tace zata iya biyansa duk irin albashin da yake buaƙata indai ya amince zai koma ƙungiyar da buga wasa.

De Bruyn, ɗan ƙasar Belgium yafara buga kakar wannan shekarar da ƙafar dama inda ya taimaka ƙungiyarsa ta City ta lashe wasanni 13 data buga sannan ta zura ƙwallaye 29 a dukkanin gasannin data buga.

A kwanakin baya ne dai ɗan wasan ya bayyana cewa  baya saurin sake kwantaragi a Manchester city domin babu inda zashi yana jin dadin buga wasa a ƙasar ta ingila.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa tuni ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG ta tuntubi wakilin ɗan wasan akan ko zasu iya samun ɗan wasan.

Ɗan wasan dai yataba buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea a shekarun baya kafin daga bisani ƙungiyar ta siyar dashi bayan ta kori Carlo Ancelotti daga aiki.

Exit mobile version