Connect with us

WASANNI

PSG Za Ta Yi Kuskuren Rabuwa Da Silva Da Cavani, Cewar Ibrahimovic

Published

on

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Zlatan Ibrahimoic, ya bayyana cewa babban kuskure PSG za tayi idan har ta bari ‘yan wasan kungiyar guda biyu, Edinson Cavani da Thiago Silva suka bar kungiyar a wannan kakar

A satin daya gabata ne aka ruwaito cewa ‘yan wasan guda biyu na shirin barin kungiyar kwallon kafan ta Paris St Germain da zarar an kammala gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a cikin watan Agusta.
Cabani, mai shekara 33 dan wasan Uruguay shi ne kan gaba a ci wa PSG kwallo da kwallaye 200 a raga, shi kuwa Silba mai shekara 35 shi ne kyaftin din kungiyar wanda shima yake fatan barin kungiyar nan gaba kadan.
Leonardo, daraktan wasanni na kungiyar PSG ya ce wannan shawara ce mai wuya da suka yanke domin dukkansu ‘yan wasan suna da tasiri a kungiyar saboda haka ba zasuji dadin matakin da suka yanke ba a matsayinsu na kungiya.
Kwantiragin ‘yan kwallon biyu zai kare ne 30 ga watan Yuni, an kuma soke gasar Faransa ta Ligue 1 a watan Afirilu, amma sai cikin watan Agusta za a karkare kofin zakarun turai na Champions League shi ya sa sai a lokacin za su bar PSG.
PSG  ta koma atisaye a jiya, 22 ga watan Yuni ta kuma kai wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League, bayan da ta doke Borussia Dortmund cikin watan Maris kafin a dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.
“Tabbas shugabannin kungiyar PSG za suyi babban kuskure idan suka bar wadannan manyan ‘yan wasan suka tafi a wannan lokacin da kungiyoyi suka shiga matsalar kudi saboda cutar Korona saboda idan ka rabu dasu kana bukatar wadanda zasu maye gurbinsu” in ji Zlatan, wanda PSG ta sayo su tare da Silba daga AC Milan.
Ya ci gaba da cewa “Yanzu akwai bukatar manyan ‘yan wasa a kungiyar wadanda zasu buga wasa da kwarewa da kuma sanin makamar aiki kuma matasan ‘yan wasan kungiyar na yanzu ba zasu iya wannan aikin ba”
Tun a watan Janairu PSG ta bukaci Cabani ya koma wata kungiyar da buga wasa bayan da Atletico Madrid ta so yin zawarcinsa, sannan aka alakanta shi da zuwa Manchester United ko Chelsea a lokacin.
A watan jiya PSG ta dauki dan wasa Mauro Icardi kan fam miliyan 54 daga Inter Milan wanda hakan yasa Cabani yake ganin ba zai samu damar buga wasanni ba da yawa idan har ya amince ya ci gaba da zaman kungiyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: