Qin Gang: Sin Ba Ta Haifar Da Matsala Ga Duniya, Sai Dai Gabatar Da Dabarun Daidaita Su

Daga CRI Hausa,

Jakadan kasar Sin dake Amurka, Qin Gang ya tattauna da mashawartan kungiyar Brookings ta Amurka, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta zaman dalilin haifar da matsaloli ga duniya, sai dai ma ta samar da dabarun daidaita matsalolin.

A cikin jawabinsa, jakada Qin ya yi tsokaci cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasashen duniya suna kara mai da hankali kan tasirin da ci gaban kasar Sin ke kawowa tsarin kasa da kasa, kuma gwamnatin Amurka ma ta bayyana sau da dama cewa, makasudin aiwatar da manufa kan kasar Sin shi ne, kiyaye tsarin kasa da kasa, sai dai, ba ta fayyace wane irin tsarin kasa da kasa ba ne.

Jakada Qin ya kara da cewa, shekaru 50 da suka gabata, aka maido da halaltacciyar kujerar kasar Sin a MDD, daga baya wato a cikin wadannan shekaru 50, a ko da yaushe, kasar Sin tana kokarin gina zaman lafiya a duniya, da taka rawa kan ci gaban duniya, da kiyaye tsarin kasa da kasa, tare kuma da samar da kayayyaki ga al’ummun duniya.

Hakazalika, Qin Gang ya yi kira da cewa, dole ne a tsai da kuduri, kuma a dauki matakai bisa hangen nesa, ta yadda za a gina kyakkyawar makoma ga kasashen Sin da Amurka, har ma ga duk duniya baki daya.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version