Connect with us

LABARAI

‘R- APC Ba Barazana Ce Ga Buhari Ba’

Published

on

Wata kungiya mai alaka da jamiyar APC a Jihar Kano mai suna Ranar wankan Buhari da Ganduje, ta kalubalanci sabon tsagin R-APC inda ta bayyana cewar wannan bangare ba ya da wata nasara wurin kawo cikas ga takarar shugaban kasa Muhammmadu buhari a zaben shekara ta 2019.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da Ganduje sun cancanci samun Kuri’a Miliyon biyar a Jihar Kano a lokacin zabe mai zuwa na shekara ta  2019 .

Shugaban Kungiyar Alhaji Bala Salihu ne ya bayyana haka a cikin wata tattunawa da akayi da wasu zababbun ‘yan jarida ranar Alhamis a Kano lokacin da yake mai da martani akan sabon bangaren R-APC wadda ke karkashin jagorancin Alhaji Buba Galadima, yace masu zabe a Kano basu da wata damuwa kan kafa Kungiyar R-APC ya kara da cewar koda kuwa ‘yan R-APC zasu fice daga APC din.Bala Dawaki ya ci gaba da cewar shirye shirye sun yi nisa na gudanar da tattakin mutane milyan uku wanda za’a gudanar a Kano da Abuja domin jaddada goyan baya ga shugaban kasa Buhari da Ganduje.

A cewar sa duk da cewa muna  kiran ‘yan bangaren R-APC da cewa kada su fita daga jam’iyya mai mulki, amman idan sun ce fita za suyi ba wanda zai matsa masu su tsaya, amma muna tabbatar masu da cewa jam’iyyar APC ba zata rufe idon ta ba akan wannan alamari, musamman idan aka dubi kyawawan ayyukan da gwamnatin Buhari da Ganduje za su ci gaba da yi idan aka sake zabarsu a shekara ta  2019.

Al’ummar Najeriya sun yarda Muhammadu Buhari ya samu gaggarumar nasara musamman a bangaren yaki da matsalar tsaro, da kuma yaki da cin hanci da rashawa, sai kuma aiwatar da manya manyan ayyuka a fadin Nijeriya.

Bugu da kari gwamnan Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu gaggarumar nasara bisa ayyuka masu mahimmanci da kuma amfani ga al’ummar Kano. Bala Dawaki ya kara da cewa tun zuwan gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje biyan albashi da kuma fanshon ma’aikata bai taba samun wani cikas ba.

Da yake karin haske kan damar Buhari ta sake cinye zaben 2019, an tabbatar da cewa  Buhari bai taba faduwa zabe a  jiharKano ba, har kuwa lokacin da yake cikin jam’iyyar adawa, balle kuma yanzu da al’ummar kasa suka ganewa idonsu manya manyan ayyukan da kuma tarin  kudaden da ya kwato daga hannun ‘yan siyasa wadanda suka sace kudade lokacin da suke kan madabun iko.
Advertisement

labarai