Zubairu M Lawal" />

Ra’ayi: Gwamna Abdullah Sule Bai Boye Tallafin Korona Ba

Gwamna Abdullah Sule

Abinda ya sanya aka kasa samun har gitsin wawushe kayan abincin tallafin annobar cutar Korona a jihar Nasarawa ba tare da an jibge jami’an tsaro a guraren rumbunar ajiyan kayan abinci ba shi ne irin tsarin rabon da Gwamna Abdullah Sule ya bi.

Farkon cutar Korona a jihar Nasarawa wanda wata mata ta shigo da shi daga balaguron da ta yi zuwa birnin Ikko, daga kanta aka fara samun masu cutar Korona a jihar Nasarawa.

Hakan ya sanya Gwamnatin ta dauki matakin takaita zurga-zurga na shiga da fice a fadin jihar.wannan matakin ya janyo an fara samun karancin abin sanyawa a haka.

Lokacin da Gwamnatin jihar Nasarawa ta fara raba kayan tallafin annobar Korona an raba shi ne bisa turban kwamishinoni da shugabannin kananan jukumomi.

Mataki na gaba da Injiniya Abdullah Sule ya dauka shine kafin a raba kayan zuwa kowace karamar hukumar sai an kiraye duk wani mai ruwa da tsaki da masu fada a ji, masamman sarakuna da shugabannin kananan hukumomi da ‘yan majalisan yan kin da Kansilolin da Kwamishinoni da masu bada shawara.

Sannan a danka kayan gare su ga kuma yan jaridu masu bayyanawa Duniya cewa Karamar Hukumar kaza ta samu kaya mota kaza cikin motar akwai kayayyaki iri kaza da kaza Kuma anmika kayan a hannun wani da wani.

Wannan kaso na biyu da Gwamna Abdullah Sule ya yi ya sanya kayan tallafin annobar cutar Korona ta samu shiga hannun mutanen jihar Nasarawa.

Kama daga Karamar Hukumar zuwa yankin raya kasa al’umman karkara sun amince da wannan kasafin kayan abincin domin ta isa garesu.

A kason kaya na uku da na hudu wanda Gwamna Abdullah Sule ya kara samun gogewa da hikima da basira da kara canza tunani. Domin ganin an tallafawa marasa galihu shine.

Kaso na uku da na hudu Gwamnan ya yi amfani da wadanan mutanen sannan aka kara da jami’an tsaro. Kuma aka bukaci duk inda aka kai kayan a tabbatar mutanin dake kulle a gida sun amfana da shi. Ba a bukatar Ma’aikatan Gwamnati ko masu Mulki su dauki kayan zuwa gidajensu domin an kawo ne zuwa ga Talakawa Fakara’ullah yan Rabbana ka wadatamu. Wadanda suke kulle a gida babu cin yau bare gobe.

Gwamna Abdullah Sule ya bude kofar kunnuwarshi domin jin koke ga duk garin da aka ji cewa kayayakin ba su shigo ba. Inda Gwamnan ya yi alkawarin duk garin da aka ce ba a kawo kayan tallafin abincin ba wadannan mutanin za su fuskanci matsala.

Wannan kiki-kakan da Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya yi wajen ganin al’umman jihar sun amfana da abincin tallafin cutar Korona ya sanya al’umman jihar suka kiyaye dokokin zaman gida a lokacin da aka kafa zaman gida da rufe kasuwanni.

Gwamnan ya samu gagarumin nasara wajen kiyaye duk abinda zai bata masa suna da muzanta Gwamnatinsa. Shi ya sanya rumbunar ajiyan kayan abinci dake cikin garin Lafia da na Shabu bai samu tarban miliyoyin matasa yan afasa kowa ya rasa ba.

Sakamkon lokacin da ake fama da annobar cutar Korona a gaban mutane ake rabom kayan zuwa kananan hukumomi, galibi matasa ke aikin dakon kayan zuwa motoci.

Gwamna Abdullah Sule ya mutumta kansa saboda wannan abinda yayi ya wanken kansa a idon Duniya da Idon Shugaban kasa Muhammad Buhari. Ya kuma wanke kansa a idon al’umman da suka raba tallafin abincin domin abiwa jama’a.

Wannan yana cikin babban nasarar da Gwamna Abdullah Sule yayi inda ya samu karbuwa wajen wasu al’umman jihar da ke ganin baya ( Action) kwatanta gaskiya da rikon Amana ya saya masa farin jini a idon al’umman jihar Nasarawa da Duniya baki daya.

Gwamnan ya kawar da kansa wajen boye kanaya abinci shi ya sanya a kokuwar da akayi na fasa runbunar abinci dake jihohi babu sunanr jihar Nasarawa kuma ba a samu kayan tallafin abinci na jihar Nasarawa a kowani shagon saya da sai dawa ba.

Wannan ba karamin karamci da mutumci Gwamnan ya samar wa kansa ba ya shiga jerin Gwamnonin da Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kara yarda da su, ya kuma jinjina masu ya amince da cewa masu kaunar jama’an jihohinsu ne.

Tunda a wannan har gitsin ba a samu Gwamna Abdullah Sule cikin Gwamnonin da suka zubra da mutumcin kansu sukayi Ambaki Bude da kayan Talakawa ba.

Exit mobile version