RA’AYI: Kiranyen Sanatan Kogi: Tsakanin Melaye Da Hukumar INEC

Daga Bode Gbadebo

Hukuncin da Mai Shari’a Nnamdi Dimgba Alkalin Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ya yanke ranar Litinin na watan 11, ga watan Satumbar 2017 cewar Hukumar Zabe ta Kasa wato INEC ta cigaba da shirye-shiryenta na yiwa Sanata Dino Melaye kiranye, bai zo da mamaki ba, idan aka yi la’akari da ganin  cewar a hakikanin gaskiya, abin da a kai wa mai karar an yi gaggawa.

Melaye, ya girmama hukuncin da kotun ta yanke sai dai, ya gwammace ya Daukaka kara. Don kaucewa taba-ba, Sanata Dino ba wai ya kai kara ne ba don dakatar da kotun cigaba da yin kiranyen ba. Dino ya yi hakan ne kawai, don bin hakkin sa a matsayin dan kasa.

A sharhi daga Teburin Edita da Jaridar Daily Trust ta buga ranar Talata ashirin da ga watan Juli na shekarar 2017 ta ce,”kai karar da Sanata Melaye a zaman sa na dan kasa yana da hakki ya je kotu.” Wannan magana gaskiya ce ta bayyana a zahiri, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da wasu jami’an sa su ne suke kara rura wutar yin kiranyen na Dino. A cewar jaridar, wasu ‘Yan Mazabar Kogi ta Yamma da aka yi wa rijista ta bayyana a zahiri, Gwamna da gwamnatin sa ne suka ingiza a yi wa Sanata Dino kiranyen, a bisa zargin ‘yan mazabar na cewa, Dino yana zama wani tarnaki ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Yahaya Bello.

Ba wanda zai iya fahimta ganin cewa a matsayin hukumar INEC, ta ci gaba da yin kiranyen na Dino, duk da cewa akwai zargin tafka almundahana a cikin lamarin.

Wani abin sha’awa shi ne, jamiyyar APC reshen Jihar Kogi ta bayyana irin wannan tsoron na cewar Hukumar INEC, ba za ta iya yin adalci ba kamar yadda ya kamata. Zai yi wuya a amince da wanda ake ganin zai hukunci da aka same shi dumu-dumu da cin hanci da rashawa, idan aka yi la’kari da zargin cin hanci da rasha na Jihar Ribas na cewar ba za a iya hukunta wanda ya taka dokokin zabe ba, kamar yin rijistar katin jefa kuri’a da wuce daya da sauran.

Bugu da kari, wani abin jin dadi shi ne, gwamnatin jihar da ta na ta kokarin nisanta kanta a kan taka rawa wajen kiranyen na Dino, sai kuma gashi abin kunya ta fito fili karara tana nuna ita ce kashin bayan tunzura yin kiranyen musamman ganin yadda kara tunzura ana yi kiranyen akwai hannun kwamishinan shari’a kuma Atoni Janar na jihar dumu-dumu a yunkurin kiranyen na Dino, inda a Babbar Kotun Tarraya lokacin da ake maganar shari’a tsakanin Dino da hukumar zaben ta kasa, ita kanta gwamnatin jihar ta Kogin, ba a sanya ta ba cikin karar ba.

Koda yake, kundin tsarin mulki na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ya baiwa ‘yan mazabar wakilai da suke da rai damar su yi wa wakilin su kiranye, amma ban da wadanda ‘yan mazabar da suka mutu.

Amma sai dai, inda Gizon ke saka shi ne, ba kowa ne zai gane mene ne ya janyo silar wannan kiranyen da ‘yan mazabar ta Sanata Dino suke son yi ba, ta hanyar karbarsa hannun da ‘yan mazabar suka yi ba da ake zargin wasu sa hannu akwai sunaye na bogi har da na wadanda suka mutu su ma sun sanya hannu don a cimma wani buri na kirayen. In har hakan ne, ya zama wajibi hukumar ta INEC, ta warware wannan matsalar, domin ta haka ne mutane za su iya ammanna da hukumar, ba kawai ta dage wajen son aiwatar da kiranyen na Sanata Dino ba.

Fiye da kokarin yi wa Sanata Dino, abin zai iya ba da wata sabuwar dama ga wasu gwamnonin kasar nan su dinga hadawa sanatocin jihohin da suke ganin makiyan su, su hada masu gadar zare don su ma a yi ma su kiranye.

Shin wai me ya sa gwamnonin mu da suka nemi kuri’un jama’a lokacin yakin neman zabe, suke nuna sun fi karfin mutane nen da suka zabe su, su yi suka a kansu? Sanata Melaye bai yi wata suka a kan Gwamna Yahaya Bello ba, shawara ya bashi a kan ya biya ma’aikata da ‘yan fansho na jihar  hakkokin su.

Gwamna Yahaya saboda wannan shawarar sai ya kulla gaba da Melaye don ya fito karara ya fadi gaskiya ta hanyar nuna damuwar sa ga halin kuncin rayuwa da ta jefa ma’aiktan da ‘yan fanshon na jihar.

Hakan, sai ya zo a kan gaba, inda shi kuma Alkali Dimgba ranar Litinin na yin watsi da takardar koken Melaye, wadda ta dai-dai da ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tawaga Sarakunan gargajiya a fadar shugaban kasa, inda Buhari ya nuna bacin ran sa, a kan yadda wasu gwamnonin jihohi suka suka yi sama da kudaden da aka tura ma su na Faris kulab don biyan wasu bukatu na musamman a jihohin su.

Har yansu gwamnonin sun kasa maida martani a kan wannan korafin na Shugaba Buhari, amma ‘yan majalisar da suka fito daga jihohi, sun kasa cewa uffan kamar yadda Dino ya yi.

Daga Bode Gbadebo, Danjarida ne daga Abuuja.

Exit mobile version