Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home Uncategorized

RA’AYI: Yaushe Talakawan Kasar Nan Za Su Ga Canjin Da Ake Kira?

by Tayo Adelaja
September 20, 2017
in Uncategorized
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Kwamared Sanusi Mailafiya

Tun daga 1999 har zuwa 2015 da jam’iyyar PDP ta mulkin kasar nan, al’ummar kasar sun tsinci kansu cikin wata dabalbalar rayuwa, inda cin-hanci da rashawa ya zama ba wani laifi ba. Jami’an gwamnatin kasar sukai ta tatike lalitar kasar nan sukai ta wadaka da almundahana su da iyalansu, yayin da su kuma talakawan kasar suka tsinci kansu cikin halin

kunci, kaka ni ka yi da kuma halin ko in kula. Babu wani bangare a kasar nan da bai fuskanci canjin fasali da kuma lalacewa ba. Harkokin ilimi, noma, lafiya, da kuma tsaro. Yayinda kuma wannan shi ne lokaci mafi samun cigaban tattalin arzikin kasar, Amma babu wani abu da talakawan suka amfana da shi tsawon wannan shekarun. PDP ta sanya al’ummar kasar cikin halin tasku, tashe-tashen hankula, tun daga fadace-fadacen Addini, kabilanci da kuma hare-haren Boko- haram. Wannan ta sanya talakawan kasar suka canza tunani suka tunbuke wannan lemar da aka kafa shekaru 16, suka zabo Shugaba Buhari, wanda talakawa ke ta

kadawa kuri’ah tun 2003, sai ga shi cikin ikon Allah ya haye karagar a jam’iyyar Tsintsiya ta APC.

Al’ummar kasar nan na kallon Shugaba Buhari, a matsayin wani jigo, mai gaskiya, wanda shi kadai ne zai iya futar da kasar daga cikin halin kuncin da take ciki, ba don komai ba sai don ganinsa tsarkakakke fiye da sauran tsoffi da sababbin Shugabannin kasar nan. Wannan ta sanya talakawan kasar sukai uwa sukai makarbiya don ganin jam’iyyun adawa irinsu ANPP, CPC da ACN sun dunkule sun haifi jam’iyyar da za ta kada PDP, kuma hakan ya faru. Tun daga lokacin kowa ke ta murna, sowa da farin ciki don ganin mai share hawayen talakawan kasar ya zo.

Sai dai daga hawansa, kowa ya zuba ido don ya ga wani irin sauyi da canji Shugaba Buhari zai kawo, kowa ya zuba ido don ya ga Shugaba Buhari ya canza kasar daga kazantacciyar kasa zuwa tsarkakakkiyar kasa. Daga barnatacciyar kasa zuwa kasa mai alkibla.

Kowa tunaninsa lokaci samun dunkulalliya kasa ya yi. Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda a tsawon shekaru biyu al’amuran suka sauya, kome ya dagule. Gwamnatin kasar

karkashin Jagora Shugaba Buhari ta janye tallafin man fetur din da talakawan ke amfana, kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi, yayin da Dalar kasar Amurka ta ninka a kan yadda Shugaban ya same ta, Cin hanci da rashawa har ga makusantan Shugaban. al’umma da yawa na ganin cewa wannan shi ne lokaci mafi zafi da suka shiga tun dawowar mukin farar hula. Wannan shi ne lokaci da talakawan kasar suke ta fafutuka da talauci, yunwa da fatara mafi muni.

Yayin da kuma talakawan ke ganin sun zabi gwamnatin ne don neman sauyi da canjin rayuwa, tare da neman samun ‘yantacciyar kasa daga hannun ‘yan jari hujja. Sai ga shi

talakawan na tambayar kawunansu “Yaushe canjin da ake kira zai zo”? Abin tambaya a nan da kuma hangen nesa nawa.

Lalle Shugaba Buhari ya zo da zuciyar gyaran, ya zo don ganin ya faranta wa talakawan da suka dangwala masa kuri’unsu. Sai dai babu yadda za a yi Shugaban ya karbi

ragamar gyaran shi kadai ba tare da taimakon al’ummar kasar ba, jami’an gwamnatin na da temakon da za su ba wa Shugaban, ‘yan majalisun kasar da kuma sauran al’ummar kasar, Kamar yadda jami’an tsaron kasar nan ke ta kokarin fatattakar ‘yan Boko – haram a yankunan Arewa maso- gabas. Kowa na da bangaren da zai taka mahimmiyar rawa don ganin mun canza zuwa daidaituwar kasa akarkashin tsarin dimokradiyya.

Lalle ne amma Shugaba Buhari yakara dagewa don ganin talakawa sun futa daga halin kuncin talauci da suke ciki. Lalle ne talakawa su ga cewa lalle Buhari Me Gaskiyan da suka zaba, bai canja ba. Kuma lalle ne Gwamnatin ta san cewa al’umma na zabar Gwamnati ne don ganin sun samu Shugabanci nagari, suna son ganin matsalar ruwa da wuta sun zama tarihi ( hakan ne zai ba wa kasashen ketare dama wajen zuba dukiyarsu a kasar ) kuma hakan ba shakka zai kara rage zaman kashe wando daga matasanmu.

Suna son ganin Gwamnati ta shinfida ayyukan raya kasa, suna son ganin harkokin ilimi, lafiya, tattalin arziki, noma da kowane bangare ya samu ci-gaba fiye da gwamnatin baya. Suna son ganin yaransu na samun ayyuka ba tare da sun ba da cin hanci da rashawa ba. Wannan kadai ita ce hanya da Talakawan kasar nan za su yadda cewa wannan gwamnatin canji ce, kuma tana kan hanyar sauya al’amuran kasar.

Lalle Gwamnatin Shugaba Buhari sai ta sauya al’amura da yawa da ke damun talakawan kasar nan, musamman yadda kayan masarufi suka yi tsada. Dole ne gwamnati ta fito da wata hanya wacce kaya za su yi sauki, sannan ya zama lalle ga gwamnatin shugaba Buhari ta yi garambawul ga majalisar zartarwa (ministoci) domin da yawansu kawai na dumama kujera ne, sannan dole ne gwamnati ta fara bincikar makusantanta musamman wadanda ake zargi da cin hanci, don takakawa su amince lalle gwamnatin kowa ce, kuma ba sani ba sabo. Wannan hanyoyi ne kadai da Gwamnatin Shugaba Buhari take da iko a kansu, kuma za ta iya zartar da su don jin dadin talakawanta.

Hausawa na cewa don tuwon gobe ake wanke tukunya, canjin tsarin gwamnati tare da girmama dimokradiyya kadai su ne mafuta don ganin an fara sauya akalar kasar. Sannan ne talakawan za su ce lalle canji ya zo. Allah ya taimaki kasarmu Nijeriya. Ameeeeen

Kwamared Sunusi Mailafiya 08036064695 (tes kawai).

 

 

 

 

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Buhari Ya Ce A Yi Sulhu Da Shugaban Koriya Ta Arewa

Next Post

Kasar Jordan Ta Baiwa Nijeriya Gudummawar Kayan Yaki

RelatedPosts

Gwamnatin Kaduna Ta Yi Wa Karnuka 6,250 Allurar Rigakafin Cutar Rabis

Gwamnatin Kaduna Ta Yi Wa Karnuka 6,250 Allurar Rigakafin Cutar Rabis

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Daga Bello Hamza, Abuja Gwamnatin jihar Kaduna ta samu nasarra...

Garkuwa

‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutum 15 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna

by Muhammad
1 week ago
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta samu nasarar kubutar da...

Caca

Caca: An Kashe Mutum Uku Akan Naira 50 A Imo

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Rabiua Ali Indabawa, An bayar da rahoton kashe samari...

Next Post

Kasar Jordan Ta Baiwa Nijeriya Gudummawar Kayan Yaki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version